Iran Ta Kai Hari Mai Muni Saudi, Ta Raunata Sojojin Amurka da Jirginsu

Iran Ta Kai Hari Mai Muni Saudi, Ta Raunata Sojojin Amurka da Jirginsu

  • Rahotanni sun nuna cewa kasar Iran ta harba makamai masu linzami wani sansanin soji a Saudiyya, inda ta raunata sojojin Amurka
  • Wani jami'in kasar Amurka ya sanar da cewa akalla sojoji 12 ne suka jikkata yayin da wasu daga cikin dakarun ke mawuyacin hali
  • Iran ta zafafa hare-haren a daren Juma'a ne bayan harin da aka kai mata kan wani kamfani, inda ta yi alawashin daukar fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Duk da maganar sulhu da shugaban Amurka, Donald Trump ke yi, Amurka/Isra'ila da Iran na cigaba da kai hare-hare ga juna.

Iran ta kai wani harin ramakon gayya kan sojojin Amurka da ke wani sansani a Saudiyya, inda ta musu ruwan makamai masu linzami.

Sojojin Amurka da jirginsu
Lokacin da aka dauko sojojin Amurka da Iran ta kashe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton New York Times ya nuna cewa harin ya biyo bayan barnar da aka yi wa Iran ne a ranar Juma'a da rana, inda ta ce ba za ta bari hakan ya tafi a banza ba.

Kara karanta wannan

Iran ta gano masu ba sojojin Amurka mafaka, ta sha alwashin ruguza su da hare hare

Iran ta raunata sojojin Amurka

Wani hari da aka kai ta hanyar makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka ya zama daya daga cikin manyan hare-haren da suka karya tsarin kariyar sararin samaniyar Amurka a cikin watan da aka shafe ana yaki da Iran.

Hari daga Iran a sansanin Prince Sultan da ke Saudiyya ya jikkata sojojin Amurka 12, biyu daga cikinsu cikin mawuyacin hali, a cewar wasu jami’an Amurka biyu da ba su da izinin yin magana a bainar jama’a.

Rahoton DW ya nuna cewa akalla jirage masu daukar tankar mai guda biyu na KC-135 mallakar Amurka ma sun lalace a harin da dakarun Iran suka kai.

Yadda ake kai hare-hare a yakin Iran

Harin ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ke sauya matsayarsa tsakanin alkawarin zaman lafiya da kuma kara tsananta hare-hare da suka shafi muhimman abubuwan more rayuwa na fararen hula.

Shugaban ya ce ana tattaunawar zaman lafiya kuma tana tafiya da kyau — wani ikirari da jami’an Iran suka karyata — duk da cewa yana kara tura jiragen ruwan yaki da dubban sojoji domin karfafa rundunar Amurka a yankin.

Kara karanta wannan

Iran ta tanadi dakaru miliyan 1 a shirin yin gaba da gaba da sojojin Amurka

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump na jawabi a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta kai hare-hare kan sansanonin Amurka a fadin Gabas ta Tsakiya a tsawon wannan yakin, tana amfani da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka masu yawa domin ramuwar gayya da kuma kawo cikas ga hare-haren Amurka.

Wadannan hare-hare sun jawo mummunar illa ga wasu sansanoni, kuma sun tilasta wa rundunar Amurka ta rarraba dubban sojoji domin kauce wa hadari, an tura wasu zuwa Turai.

Ana shirin sasanta Iran da Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wasu kasashe uku sun fara tsara yadda za a kawo karshen yakin Amurka da Iran da ya shafe kwana 30 ana barin wuta.

Rahotanni sun nuna cewa Pakistan, Masar da Turkiyya ne suka shirya jan ragamar sulhu domin dawo da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Sun fara kokarin hakan ne yayin da Donald Trump ke cewa ya tattauna da kasar Iran tare da gindaya wasu sharuda da ya ce ya kamata Tehran ta amince da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng