Iran Ta Yi Babban Kamu, an Gano Mutane da Ke Yada Sirrinta ga Makiya a Yaki da Isra'ila
- Hukumomin Iran na ci gaba da samun nasara a yakin da suke yi da ƙasar Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya
- Ƙasar ta cafke wasu mutane akalla 15 a Isfahan bisa zargin aika muhimman bayanai zuwa kafafen yada labarai
- Rahotanni sun ce ana zargin wadanda aka kama da bayyana wuraren sojoji da kuma hotunan barnar hare-hare ga wasu hanyoyin sadarwa na waje
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ana ci gaba da gwabza yaki tsakanin Iran da kuma kasar Isra'ila da ke samun tallafin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da samun nasara a Iran musamman kan masu yada bayanan sirrinta ga makiyanta.

Source: Facebook
Hukumomin Iran sun cafke akalla mutane 15 a lardin Isfahan bisa zargin aika muhimman bayanai zuwa kafafen yada labarai, cewar Al Jazeera.
Iran na samun galaba kan masu leken asiri
Ko a kwanakin baya ma, Iran ta tabbatar da kama wani dan Isra'ila da ake zargin yana yada bayananta na sirri da abokiyar fadanta a yakin da ake yi.
Kasar ta sanar da kama mutumin da ke yi wa Isra’ila leƙen asiri ta hanyar ba da hotuna da bayanai masu muhimmanci da ake yada su da wasu makiyanta.
An kama shi a lokacin rikicin kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra’ila wanda ke ƙoƙarin mamaye Gabas ta Tsakiya bayan tsoma bakin Amurka wacce ke tallafa wa abokiyar gabarta.
Rahotanni sun ce an ɗauki ɗan leƙen asirin aiki ta yanar gizo yayin da yake Sweden, inda ya zo aikin sa ido a Iran tare da kawo mata cikas a yakin da ake yi.

Source: Getty Images
Yadda ake yada bayanan sirrin Iran ga makiya
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana tura bayanan ne ga kafofin yada labarai da gwamnatin Tehran ke kallon masu adawa da ita da kuma kawo mata cikas a yakin da ake yi.
A cewar wata majiya, an zargi mutanen da yada bayanan sirri kamar wuraren sansanonin sojoji da kuma hotunan barnar hare-hare ga wasu kafafe.
Rahoton ya bayyana cewa wadannan bayanai sun hada da muhimman bayanai da ka iya zama hadari ga tsaron kasa da kuma kokarin gwamnati na kare kanta.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da ake kokarin gano yadda bayanan suka fita da kuma mutanen da ke da hannu, kamar yadda Middle East Eye ta ruwaito.
Iran/Isra'ila: Ana zargin yan Najeriya da leken asiri
A labari mai kama da wannan, an ji cewa wani shaida na hukumar DSS, ya fada wa kotu cewa wasu da ake zargi da ta’addanci sun amsa laifin leken asiri.
Mutumin ya tabbatar da cewa mutanen uku sun yi leƙen asiri kan ofisoshin jakadancin Amurka da Isra’ila a yakin da ake yi.
Ya ce wadanda ake tuhuma uku sun bayyana cewa sun je Iran domin samun horo kan makamai da tattara bayanan sirri kafin dawowa Najeriya.
Asali: Legit.ng

