Iran Ta Tanadi Dakaru Miliyan 1 a Shirin Yin Gaba da Gaba da Sojojin Amurka

Iran Ta Tanadi Dakaru Miliyan 1 a Shirin Yin Gaba da Gaba da Sojojin Amurka

  • Dakarun kasar Iran na kara shirye-shiryen fuskantar Amurka yayin da yakin da suke ya ke kara tsananta duk da maganar sulhu da aka fara
  • Shugaban Amurka, Donald Trump na kara tura daruruwan sojoji Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke nuna cewa akwai wani shiri da yake yi
  • A daya bangaren, gwamnatin Iran ta tanadi dakaru sama da miliyan daya domin zaman shiri ko-ta-kwana idan Amurka ta ce za ta shiga kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rahotannin da ke fitowa daga Tehran na nuna cewa gwamnatin Iran ta fara wani shiri na musamman domin gwabzawa da sojojin Amurka.

Hakan na zuwa ne yayin da sojojin Amurka ke kara tafiya Gabas ta Tsakiya a shirin kai farmaki Iran tun bayan fara yakin da suka yi.

Kara karanta wannan

Duk da gargadin Iran ga Trump, Amurka ta yi biris kan matakin da ta shirya dauka

Dakarun sojoji Iran
Sojojin Iran na fareti a gaban marigayi Ayatollah Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Times of India ya nuna cewa an tambayi Donald Trump kan shirin tura sojojin kasa Iran a wata hira da ya yi, inda ya bayar da amsa mai harshen damo.

Iran ta tanadi sojoji miliyan 1

An ruwaito cewa cibiyoyin ɗaukar ma’aikata da ke da alaƙa da Basij, dakarun IRGC, da kuma rundunar sojin Iran sun kara daukar mutane sosai, inda matasa da dama ‘yan Iran suka fito suna nuna shirinsu na shiga kare ƙasar.

Haka kuma, an ruwaito cewa Iran na ƙarfafa ayyukanta a tsibirin Kharg a ‘yan makonnin nan, inda ta tura ƙarin sojoji da tsarin kariyar sama, tare da kafa wasu dabarun tsaro.

Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi gargadi a ranar Laraba ga maƙiyan ƙasar da kada su yi yunƙurin mamaye tsibiran Iran, yana mai nuni da yiwuwar wasu abubuwa da ke faruwa a yankin.

“Bisa wasu bayanai, maƙiyan Iran tare da taimakon wata ƙasa a yankin suna shirin mamaye ɗaya daga cikin tsibiran Tehran,”

Kara karanta wannan

Ana zargin Rasha ta kusa kammala aika jiragen yaƙi marasa matuƙa ga Iran

Inji Ghalibaf a wani saƙo da ya wallafa a dandalin X.

Ya ƙara da cewa:

“Dukkan motsin maƙiya na ƙarƙashin cikakken sa ido na rundunoninmu.”

Gargadi ga kasashen Larabawa

Ya gargadi cewa idan suka wuce gona da iri, duk muhimman cibiyoyin wata ƙasa a yankin za su zama abin da za a kaiwa hari nan take.

Wani rahoto ya ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya shaida wa mashawartansa cewa yana son kauce wa yaƙi mai tsawo a Iran, kuma yana fatan kawo ƙarshen rikicin cikin makonni masu zuwa.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na yi wa Amurkawa jawabi a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahotanni na baya sun nuna cewa Ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta riga ta tsara cikakkun shirye-shirye na yiwuwar tura sojojin ƙasa zuwa Iran.

Sai dai da aka tambaye shi game da yiwuwar tura sojoji a ranar Alhamis, Trump ya ce:

“A’a, ba zan tura sojoji ko’ina ba,”

Amma ya ƙara da cewa:

“Idan zan yi hakan, ba zan gaya muku ba,”

Isra'ila na fuskantar matsalar soja

A wani labarin, kun ji cewa Babban hafsun sojar kasar Isra'ila ya fito ya yi korafi game da barazanar da suke fuskanta yayin yaki da Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta yi gargadi ga Amurka kan tura sojoji, ta fadi sakamakon da zai biyo baya

Hafsun sojojin ya sanar da cewa rundunar sojin kasar za ta iya rugujewa saboda karancin ma'aikata, inda ya bukaci a dauki matakin gaggawa.

Wasu 'yan adawa a kasar sun fara sukar gwamnatin Benjamin Netanyahu, inda suka bukaci a rika daukar jama'a soja domin cike gibin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng