Ana cikin Gwabza Yaki, Trump Ya Fasa Kwai kan Babbar Kyautar Iran ga Amurka

Ana cikin Gwabza Yaki, Trump Ya Fasa Kwai kan Babbar Kyautar Iran ga Amurka

  • A kwanakin baya Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa Iran ta ba da babbar kyauta wadda darajarta ta kai ta miliyoyin kudi
  • Donald Trump ya fito ya ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026 ya bayyana wace irin kyauta Iran ta yi bayan ya bar jama'a cikin duhu
  • Shugaban na Amurka ya bayyana cewa Iran ta ba da kyautar ne domin nuna cewa da gaske take yi game da tattaunawa don kawo karshen yakin

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya warware zare da abawa kan babbar kyautar da ya ce Iran ta yi.

Donald Trump ya ce Iran ta amince jiragen dakon mai 10 su ratsa ta mashigar ruwa ta Hormuz a matsayin "kyauta" domin nuna cewa da gaske take game da tattaunawar kawo karshen yakin.

Kara karanta wannan

Trump ya faɗi abin da Iran ta bukata a gare shi a yaki, ya kara mata wa'adin kwanaki 10

Trump ya bayyana kyautar da Iran ta ba Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na magana a gaban jirgi Hoto: Roberto Schmidt
Source: Getty Images

Jaridar The Hill ta ce Shugaba Donald Trump ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026.

Wace kyauta Trump ya ce Iran ta yi?

Trump yana nufin wasu kalaman boye ne da ya yi kwanaki biyu baya game da wata "kyauta" daga Tehran wadda ta shafi zirga-zirgar mai da iskar gas ta mashigarruwan, wadda take babbar hanyar kasuwancin makamashi na duniya.

Dakarun Iran sun dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar kusan gaba daya tun bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya kusan makonni hudu da suka gabata.

"Sun ce, 'Domin nuna muku cewa mu din na gaske ne kuma muna nan daram, za mu bari ku samu jiragen ruwa na mai guda takwas."

- Donald Trump

Jiragen ina ne aka bari suka wuce?

Trump ya ce ya yi amanna cewa jiragen dakon man na kasar Pakistan ne, inda ya kara da cewa ya ga rahotannin labarai da ke nuna cewa sun wuce ta mashigar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Trump ya fasa kwai, ya bayyana abin da jagororin Iran ke tsoro

"Sai na ce, 'To, ina ganin muna tattaunawa da mutanen da suka dace.' Kuma a zahiri ma, sai suka ba da hakuri kan wani abu da suka fada, sannan suka ce, 'Za mu sake tura wasu jiragen ruwa guda biyu.'"

- Donald Trump

Kafin ya ba da wannan bayanin ga manema labarai, Trump ya fara tambayar mai shiga tsakani a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, a teburin taron inda ya ce, "Steve, ko zan iya bayyana kyautar?"

Shugaban na Amurka bai bayar da wasu karin bayani ba.

Wadanne kasashe jiragen suka nufa?

Tashar Channels tv ta ce bayanai daga kamfanin binciken teku na Kpler sun nuna cewa jiragen dakon mai guda shida da na iskar gas guda biyar ne suka ratsa Tekun Fasha tun ranar Litinin.

Trump ya ce Iran ta ba da kyauta
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Amma ba a samu wani tabbaci mai zaman kansa da ke nuna cewa su ne wadanda Trump ya ambata ba.

Daga cikin wadannan jiragen, jiragen dakon mai uku da na iskar gas biyu a halin yanzu suna karkashin takunkumin Amurka ne da ya shafi Iran.

Bisa ga alamun bin diddiginsu, biyu daga cikin jiragen dakon mai shidan sun nufi kasar China ne, yayin da daya kuma ya nufi kasar Thailand.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta yi abin da ba a yi tsammani ba, ta nemi alfarmar Trump kan Iran

Daga cikin masu dauke da iskar gas, daya yana kan hanyar zuwa Singapore yayin dayan ya riga ya isa kasar India. Sauran jiragen guda shida ba a samu bayanan inda suka nufa ba.

Iran ta shirya mamayar Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun musamman na Iran sun fara wani muhimmin shiri kan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Manyan sojojin na Iran da suka ƙunshi dakarun runduna ta 65 ta Airborne ta rundunar sojoji, wadda aka sani da NOHED, suna shirye-shirye don kai wa Amurkawa babban hari.

Dakarun na NOHED za su kai hare-haren a wani aikin haɗin gwiwa da dakarun musamman na Saberin na rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng