Trump Ya Faɗi Abin da Iran Ta Bukata Gare Shi a Yaki, Ya Kara Mata Wa'adin Kwanaki 10
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana kan tattaunawa da Iran, ya kara wa’adin Iran bude mashigar Hormuz
- Isra’ila ta ce ta kashe kwamandan rundunar ruwa ta Iran, yayin da hare-hare suka karu, Iran na ci gaba da mayar da martani a yankin Gabas ta Tsakiya
- Ana fuskantar kalubale wajen cimma yarjejeniya, yayin da Amurka da Iran ke musayar zarge-zarge, kuma rikicin na kara fadada zuwa kasashe da dama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Donald Trump na Amurka ya kara wa’adin da ya bai wa Iran na bude mashigar Hormuz da kwanaki 10.
Hakan na zuwa ne bayan ya ce tattaunawa na tafiya yadda ya kamata sosai ba tare da wata matsala ba.

Source: Twitter
Trump ya kara wa Iran wa'adin kwana 10
Trump ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social a yau Alhamis 26 ga watan Maris, 2026.
Ya ce bisa bukatar gwamnatin Iran, ya dakatar da shirin lalata cibiyoyin makamashi na tsawon kwanaki 10 har zuwa ranar 6 ga Afrilu, 2026 da misalin karfe 8:00 na dare agogon Gabashin Amurka.
Tun da farko, Trump ya bukaci shugabannin Iran su amince da tattaunawa domin kawo karshen rikicin da ya shafe kusan wata guda, ko kuma su fuskanci karin hare-hare kan manyan jami’ansu.
A gefe guda, Isra’ila ta sanar da kashe kwamandan rundunar ruwa ta IRGC mai suna Alireza Tangsiri tare da wasu manyan jami’ai a wani hari da aka kai tashar Bandar Abbas.
Rahotanni sun ce an kai hare-hare masu tsanani a yankin Isfahan, wanda ke dauke da sansanin soji da kuma daya daga cikin cibiyoyin nukiliya da Amurka ta kai hari a baya.
Sai dai Iran ta musanta cewa tana rokon a yi yarjejeniya kamar yadda Trump ya fada, inda ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya a yankuna daban-daban na Gabas ta Tsakiya.

Source: Twitter
Trump ya fadi kyakkyawar niyyar Iran
Trump ya kuma yi gargadin cewa idan Iran ba ta sauya matsayinta ba, za ta fuskanci matsin lamba mai tsanani, yana mai cewa Amurka na da karfin da zai zama mafarki mai ban tsoro ga Tehran.
Ya kuma yi ikirarin cewa Iran ta bari jiragen mai guda 10 su ratsa mashigar Hormuz a matsayin alamar kyakkyawar niyya a yayin tattaunawar da ake yi.
A bangaren Iran, ministan harkokin wajen kasar, Abbas Araghchi ya zargi Amurka da nuna son kai, yana cewa dokar kasa da kasa ba ta zama abin amfani ga wasu kawai ba.
Rahotanni sun nuna cewa Pakistan na taka rawa a matsayin mai shiga tsakani, inda aka bukaci Amurka ta tabbatar da tsaron wasu manyan jami’an Iran yayin tattaunawa.
Wani jami’in Iran ya bayyana shirin Amurka na kawo karshen rikicin a matsayin wanda bai dace ba, amma ya ce ana ci gaba da kokarin diflomasiyya tsakanin bangarorin.
Trump ya gargadi Iran kan sharudan zaman lafiya
A wani labarin, shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargadi mai tsauri ga hukumomi a Iran kan bijirewa sharudan zaman lafiya.
Trump ya yi barazanar cewa idan Iran ta ki amincewa da wadannan sharuda, matakin Amurka zai tsananta kuma 'ba zai yi kyau ba'.
Trump ya kuma soki NATO yana cewa kasashen kungiyar ba su taimaka ba a yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila.
Asali: Legit.ng

