Wata Sabuwa: Trump Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Abin da Jagororin Iran Ke Tsoro
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya hakikance cewa kasarsa na tattaunawa da Iran kan yakin da ake yi
- Donald Trump ya bayyana cewa akwai dalilin da ya mahukunta a Iran suka ki amincewa a fili suna tattaunawa da Amurka
- Shugaban kasar na Amurka ya kuma yi wa 'yan jam'iyyar Democrat shagube kan sukar da suke yi a kan yakin da ake yi a Iran
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada a ranar Laraba cewa Iran ta shiga cikin tattaunawar zaman lafiya.
Trump ya bayyana cewa musantawar da Tehran ke yi ya faru ne saboda masu tattaunawar na Iran suna tsoron kada mutanensu su kashe su.

Source: Getty Images
Jaridar Strait Times ta ce Trump ya bayyana hakan ne yayin wani taron cin abincin dare da 'yan majalisar jam'iyyar Republican a ranar Laraba, 25 ga watan Maris 2026.
Me Trump ya ce kan Iran?
"Suna tattaunawa, a zahiri ma, kuma suna son kulla yarjejeniya sosai. Amma suna tsoron fadar hakan, saboda suna ganin mutanensu za su kashe su."
"Suna kuma jin tsoron cewa mu ne za mu kashe su."
Kalaman shugaban na Amurka sun zo ne bayan da Ministan harkokin wajen Iran, abbas Araghchi ya bayyana cewa "ba mu da niyyar yin tattaunawa".
Trump ya yi shagube ga 'yan Democrat
Trump ya sake nanata ikirarinsa na cewa ana "ragargaza" Iran a rikicin da yanzu haka ya shiga mako na hudu, duk da cewa Tehran har yanzu tana da iko mai karfi kan mashigar ruwa ta Hormuz wadda take hanyar jigilar mai.
Yayin da yake sukar abokan hamayyarsa na cikin gida, Trump ya kuma yi ikirarin cewa 'yan jam'iyyar Democrat suna kokarin "karkatar da hankali daga gagarumar nasarar da muke samu a wannan aikin sojan."
Cikin sako na izgili game da kiran da 'yan Democrat ke yi masa na ya nemi amincewar Majalisa kafin yaki, Trump ya kara da cewa:
"Ba su son kalmar 'yaki,' saboda ya kamata ka samu amincewa, don haka zan yi amfani da kalmar 'aikin soja'."
Trump ya shirya daukar mataki kan Iran
Tashar RTE ta ce tun da farko fadar White House ta bayyana cewa Trump a shirye yake ya dauki kwakkwaran mataki idan Iran ba ta amince da shan kashi ba, yayin da take jaddada cewa Tehran har yanzu tana shiga cikin tattaunawa.
Mai magana da yawun bakin fadar White House, Karoline Leavit ta bayyana cewa:
"Idan Iran ta kasa amincewa da gaskiyar halin da ake ciki yanzu, idan suka kasa fahimtar cewa an yi nasara a kansu ta fuskar soja kuma za a ci gaba da yin hakan, Shugaba Trump zai tabbatar da cewa an ragargajesu fiye da yadda aka taba yi a baya."
"Shugaba Trump ba ya wasa kuma a shirye yake ya sakko da jahannama. Bai kamata Iran ta sake yin kuskuren lissafi ba."

Source: Getty Images
Lokacin da aka tambaye ta ko tattaunawa da Iran ta tsaya cik, Leavitt ta amsa da cewa:
"Tattaunawa na ci gaba. Kuma tana samar da sakamako."
Trump na son kawo karshen yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya fara kosawa kan yakin da ake yi da Iran.
Donald Trump, ya shaida wa mashawartansa cewa yana son a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran cikin gaggawa.
Shugaban na Amurka na kokarin kammala rikicin cikin makonni kaɗan masu zuwa domin fuskantar wasu abubuwa na musamman.
Asali: Legit.ng


