Isra'ila Ta Shammaci Iran, Ta Hallaka Babban Kwamandan Sojoji
- Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) na ci gaba da yin dauki dai-dai ga manyan jagorori da kwamandojin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- IDF ta sake hallaka wani babban kwamandan sojojin ruwa na rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC)
- Rundunar IDF ta kashe Alizera Tansgiri ne a wani hari da ta kai yayin da yake ganawa da da wasu jami'an sojojin ruwa na Iran
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - An kashe babban kwamandan sojojin ruwa na rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), Alireza Tangsiri.
An kashe Alireza Tansgiri ne a wani harin Amurka da Isra'ila a yankin gabar teku na Bandar Abbas.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton kashe babban kwamandan a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026.
Isra'ila ta kashe Alireza Tansgiri

Kara karanta wannan
Ba sassauci: Iran ta ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila, ta farmaki muhimman wurare
Alireza Tangsiri ne ke da alhakin rufe mashigar ruwa na Hormuz, a cewar rahoton jaridar Times of Israel.
Har yanzu dai babu wani martani daga kasar Iran kan kisan. Idan har aka tabbatar, wannan zai zama babban rashi na baya-bayan nan na wani babban jami'i a yakin da yanzu haka yake mako na hudu.
Tangsiri yana daya daga cikin kalilan din manyan jami'an gwamnatin Iran da suka tsira daga yunkurin kisan gilla na Amurka da Isra'ila ya zuwa yanzu.
Kwararren kwamanda ne da ke kan mukamin tun shekarar 2018, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen rufe mashigar ruwa ta Hormuz da Iran ta yi.
Isra'ila ta aika sako ga jagororin Iran
Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya tabbatar da kashe Alireza Tansgiri yayin wani taron bita na safe tare da jami'an soja.
"Rundunar IDF ta kawar da kwamandan rundunar sojojin ruwa ta IRGC, mutumin da ke da alhakin kai-tsaye kan ayyukan ta'addanci na dasa bama-bamai da toshe mashigin ruwa na Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa."

Kara karanta wannan
Jagorori da kwamandojin Iran 10 da aka kashe tun bayan fara yaki da Amurka, Isra'ila
Katz ya ce harin wani "sako" ne ga IRGC: "IDF za ta farauto ku sannan ta kawar da ku daya bayan daya."
"Za mu ci gaba da gudanar da ayyuka a Iran da dukkan karfinmu domin cimma manufofin yakin."
- Israel Katz
An farmaki Alireza Tangsiri ne a birnin Bandar Abbas na kasar Iran yayin da yake ganawa da manyan kwamandojin rundunar sojojin ruwa ta IRGC, a cewar jami'an Isra'ila.

Source: Twitter
Isra'ila ta kashe manyan jagorori a Iran
An kashe tsohon jagoran addini na Iran da wasu manyan mutane da dama da kwamandojin dakarun kare juyin juya hali a hare-haren Amurka da Isra'ila.
Amma gwamnatin kasar ta ci gaba da rike ikonta na tsara dabaru da gudanar da ayyuka a yakin da aka fara ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Iran ta karyata Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukunta a Iran sun karyata ikirarin Donald Trump na fara tattaunawa kan yakin da ake yi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei ya yi watsi da ikirarin shugaban kasar na Amurka kan batun tattaunawa.
Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa babu wata tattaunawa da Iran za ta shiga da Amurka saboda ta yi a baya ba ta ji dadi ba.
Asali: Legit.ng