Yakin Iran Ya Kawowa Trump Cikas kan Muhimmin Abin da Ya Tsara da China
- Bata kashi da aka shafe sama da mako uku ana yi tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran ya kawo matsala kan shirin Donald Trump na zuwa China
- Shugaban Amurka ya sanar da sabuwar ranar da zai ziyarci Xi Jinping na kasar China, inda ya ke fatan gama yaki da Iran kafin lokacin
- Rahotanni sun bayyana cewa wannan ne karon farko da Shugaban kasar Amurka zai ziyarci kasar China a kusan shekaru 10 da suka gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai gana da shugaban ƙasar China, Xi Jinping, a ranakun 14 zuwa 15 ga watan Mayun 2026.
Hakan na zuwa ne bayan da aka jinkirta muhimmiyar ziyarar Trump zuwa China sakamakon yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa wannan ne zai kasance karo na farko cikin kusan shekaru 10 da wani Shugaban Amurka zai ziyarci kasar China.
Donald Trump zai tafi China a Mayu
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta tabbatar da ranakun ziyarar a Mayun 2026, tana mai cewa Shugaba Xi ya fahimci halin da ake ciki kuma ya amince da buƙatar jinkirta tafiyar.
Ta ce:
“Shugaba Xi ya fahimci cewa yana da matuƙar muhimmanci shugaban ya kasance a gida yayin waɗannan ayyukan yaƙi da ake yi a yanzu.”
Reuters ta ce ana sa ran Trump zai karɓi baƙuncin Xi a birnin Washington DC daga baya a wannan shekarar, inda ya ce jami’ai na kammala shirye-shiryen waɗannan muhimman ziyarce-ziyarcen.
Kasar China ba ta yi martani ba
Har yanzu Beijing ba ta mayar da martani kan ranakun da Trump ya bayyana ba, domin ba ta saba bayyana jadawalin ayyukan shugabanta da wuri ba.
Sai dai ma’aikatar harkokin wajen China ta bayyana a baya cewa tana tattaunawa da Amurka kan lokacin ziyarar shugaba Donald Trump.

Source: Getty Images
An tsara wannan tafiya tun da farko a ranar 31 ga Maris, 2026 amma aka jinkirta ta bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da manyan hare-hare kan Iran a watan da ya gabata.
A matsayin martani, Iran ta kai hare-hare kan Isra’ila da ƙasashen da ke kawance da Amurka a yankin Tekun Fasha, tare da kusan rufe mashigar Hormuz.
Trump ya je China a shekarar 2017
Lokaci na ƙarshe da wani shugaban Amurka ya ziyarci China shi ne a watan Nuwamban 2017, a lokacin wa’adin mulkin farko na Trump.
Haka kuma ganawa ta ƙarshe tsakanin Trump da Xi ita ce a watan Oktoban 2025 da ya gabata a Koriya ta Kudu, a wajen taron APEC.
Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta dade tana fuskantar matsaloli, tun daga rikicin kasuwanci zuwa fafatawar fasaha da kuma takaddama ta siyasa.
Shugaban Amurka na son gama yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Donald Trump na son kawo karshen yakin da Amurka da Isra'ila suka fara da kasar Iran.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Donald Trump ya sanar da wasu hadimansa da cewa su dauki matakan kawo karshen yakin cikin gaggawa.
Wata majiya daga White House ta ce daga cikin dalilan da suka sanya Trump son kammala yakin akwai shirinsa na zuwa kasar China.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


