Lissafi na Neman Kwacewa: Trump na Son Gama Yaki da Iran cikin Gaggawa
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya fara kira ga jami'an gwamnatinsa da su kawo karshen yaki da a yanzu haka suke yi da kasar Iran
- Donald Trump na son ganin yakin ya kare ne domin samun damar cigaba da wasu muhimman abubuwan da ya tsara a watannin baya
- A halin da ake ciki dai yakin na cigaba da daukar zafi, inda Isra'ila ta sanar da cewa Iran na cigaba da harba mata makamai masu linzami
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - An ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya shaida wa mashawartansa cewa yana son a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran cikin gaggawa.
Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin shiga mako na hudu da fara yakin ba tare da kawo karshensa ba duk da an fara maganar tsagaita wuta.

Source: Getty Images
Trump na son gama yakin Iran
Jaridar Wall Street Journal ta ce Donald Trump na kokarin kammala rikicin cikin makonni kaɗan masu zuwa domin fuskantar wasu abubuwa na musamman.
A cewar majiyoyin fadar White House, Trump na son a dakatar da faɗan kafin ranar 14 ga Mayu, lokacin da ake sa ran zai gana da shugaban China, Xi Jinping, a birnin Beijing domin tattaunawar da aka jinkirta sakamakon yaƙin.
Trump ya sha bayyana cewa hare-haren haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran, waɗanda suka fara a watan da ya gabata, na gab da cimma manufofinsu.
Sai dai masu adawa da shi kan yakin na cewa gwamnatinsa ba ta bayyana waɗannan manufofi a fili ba ko kuma yadda za a cimma su.
Hakan na zuwa ne bayan Iran ta yi ba’a ga shirin sulhun da Fadar White House ta gabatar a ranar Laraba, tana mai cewa za ta kawo ƙarshen yaƙin bisa sharudan kanta.
Alamar yakin zai dauki lokaci
Martanin Iran ya nuna cewa har yanzu tsagaita wuta a yakin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 1,000 tare da girgiza tattalin arzikin duniya ba zai zo karshe nan kusa ba.
Tehran ta ce tana nazarin shirin sulhu bisa sharudan Trump 15, amma ta nuna rashin amincewa da yiwuwar tattaunawa da Washington.

Source: Getty Images
Amurka ta bukaci Iran ta daina haɓaka sinadarin nukiliya, ta rage samar da makamai masu linzami, sannan ta sake buɗe mashigar Hormuz.
Iran ta harba makamai Isra'ila
Sojojin Isra’ila sun ce tsarin kare sararin samaniya na ƙasar na aiki domin dakile hare-haren makamai masu linzami daga Iran da safiyar Alhamis.
Rahoton jaridar Telegraph ya nuna cewa an kunna ƙararrawa a Isra’ila ta Tsakiya, wasu sassan Jerusalem, da kuma yankin Yammacin Kogin Jordan domin a ankara da hare-haren Iran.
Fafaroma ya nemi tsayar da yaki
A wani labarin, kun ji cewa Fafaroma Leo ya yi magana kan yakin da ake tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya yi kira ga dukkan kasashen da ke cikin yakin da su koma teburin sulhu domin kawo karshen rikicin maimakon amfani da makamai.
Fafaroman ya sanar da cewa ba za su zuba ido suna gani ana cigaba da kai hare-hare ana kashe fararen hula da raba su da gidajensu a duniya ba.
Asali: Legit.ng


