Ana tsakiyar Musayar Wuta, Iran Ta Samu Gagarumin Goyon Baya a Yaki da Amurka
- Firayim Minista Anwar Ibrahim ya yaba wa Pakistan kan yunkurin shiga tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya
- Malaysia ta jaddada cewa Iran tana da hakkin kare kanta karkashin dokokin kasa da kasa yayin da Isra'ila ke kai mata hare-hare ba kakkautawa
- Anwar ya yi kira ga manyan kasashen duniya da su daina nuna son zuciya wajen amfani da dokokin duniya ta hanyar goyon bayan bagare daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Malaysia - Firayim Ministan ƙasar Malaysia, Anwar Ibrahim, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tayin da ƙasar Pakistan ta yi na karɓar bakuncin tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran.
Anwar ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin wanda ya zo a daidai gaba, duba da yadda takaddama ke ƙara ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Malaysia na tare da Iran a yaki da Amurka
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 25 ga Maris, 2026, Anwar Ibrahim ya yaba wa takwaransa na Pakistan, Shehbaz Sharif, kan yadda ya nuna jajircewa wajen buɗe ƙofar diflomasiyya a wannan mawuyacin lokaci.
Ya bayyana cewa:
“Matsayin Pakistan a duniyar Musulmi da kuma dangantakarta da ɓangarorin da abin ya shafa, ya ba ta damar samar da yanayi mai kyau na tattaunawa.”
Baya ga goyon bayan sulhun, Malaysia ta sake jaddada matsayinta na goya wa Iran baya na kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra'ila.
Anwar ya bayyana cewa:
“Malaysia ta tabbatar da haƙƙin Iran na kare ikon ƙasarta, kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka amince da shi, musamman duba da hare-haren Isra'ila da ake ci gaba da kai wa a ƙasar da kuma Lebanon.”
Malaysia ta aika sako ga Iran da Amurka

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Iran ta yi martani kan ikirarin Trump na fara tattaunawa kan yakin da ake yi
Duk da haka, Firayim Ministan ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da su nuna matuƙar kamun kai domin tabbatar da cewa ba a jawo farar hula da sauran ƙasashen yankin, musamman ƙasashen Tekun Fasha, cikin wannan rikici ba.
Ya jaddada cewa tattalin arziki da zaman lafiyar duniya suna fuskantar babban haɗari idan har aka bar yaƙin ya faɗaɗa fiye da yadda yake yanzu.
Anwar Ibrahim ya soki yadda wasu ƙasashe ke amfani da dokokin ƙasa da ƙasa ta hanyar son zuciya. A cewarsa, yarda da tsarin dokokin duniya ya dogara ne kan yin adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Kokarin Pakistan a yakin Gabas ta Tsakiya
A game da hakan, Anwar Ibrahim ya ce:
“Dokokin ƙasa da ƙasa ba za su iya zama garkuwa ga ɓangare ɗaya da yaki bin doka ba, yayin da ake hana ɗayan bangaren haƙƙinsa na kare kansa.”
A kwanakin nan, Anwar ya bayyana cewa ya tattauna da shugabannin ƙasashen Turkiyya, Masar, Indonesia, Japan, da Pakistan domin neman hanyoyin kwantar da tarzoma.
Malaysia ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da mara baya ga duk wani yunkuri na gaskiya, wanda zai kai ga samar da adalci da zaman lafiya mai dorewa a duniya.
Asali: Legit.ng
