Iran Ta Saki Bidiyon Lokacin da Ta Harba Makami zuwa Isra'ila da Barnar da Ya Yi

Iran Ta Saki Bidiyon Lokacin da Ta Harba Makami zuwa Isra'ila da Barnar da Ya Yi

  • Akalla mutane 16 ne suka mutu a yau Talata sakamakon harin makaman linzami da kasar Iran ta kaddamar kan biranen Tel Aviv yau.
  • Hukumar agajin gaggawa tana kokarin ceto mutanen da suka makale a karkashin baraguzan gine-ginen da suka ruguje a birnin Tel Aviv a yau.
  • Sojojin Isra'ila sun mayar da martani ta hanyar kai hari kan wurare hamsin a cikin kasar Iran a daren yau Talata yayin yakin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila - A safiyar ranar Talata, 24 ga Maris, 2026, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) suka ƙaddamar da jerin gwanon hare-haren makamai masu linzami kan ƙasar Isra'ila.

Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa aƙalla mutane 16 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon waɗannan hare-hare.

Iran ta harba jerin gwanon makamai kan ksar Isra'ila.
Wani makami mai linzami kirar Shahab-3 da Iran ta harba a wani yankin sahara. Hoto: SHAIEGAN/FARS NEWS/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta harba tarin makamai zuwa Isra'ila

Kara karanta wannan

An yi ruwan makamai a Tel Aviv, Isra'ila ta fadi barnar da harin Iran ya yi mata

Rahoton da CNN ta fitar ya nuna cewa waɗannan makamai na Iran sun daki manyan biranen Isra'ila ciki har da Tel Aviv da kuma yankin Dimona dake kusa da cibiyar binciken makamashin nukiliya ta Negev.

Tun da tsakar dare, Iran ta kaddamar da jerin gwanon hare-hare guda bakwai, kuma da yawan makaman sun fada kan abin harinsu ba tare da shamaki ba.

Hotuna da faifan bidiyo da dakarun Iran suka fitar sun nuna yadda aka riƙa harba makaman, yayin da a sararin samaniyar Isra'ila kuma aka riƙa ganin yadda garkuwar soja ke ƙoƙarin kakkabe su.

Sai dai, wasu makaman sun samu nasarar faɗawa cikin birane, inda suka haddasa rugujewar gine-gine da lalacewar motoci, tare da jawo tashin gobara.

Barnar da harin Iran ya yi a birnin Tel Aviv

A birnin Tel Aviv, wani babban ginin mutane mai hawa da dama ya ruguje, inda rahotanni suka nuna cewa akwai fararen hula da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.

Hukumar agajin gaggawa ta Magen David Adom (MDA) ta bayyana cewa:

“Aƙalla wurare huɗu ne makaman suka daka a cikin Tel Aviv, inda ya zuwa yanzu aka samu mutane shida da suka jikkata.”

Kara karanta wannan

An fitar da bidiyon yadda rokokin Iran suka ruguza Isra'ila

Jami'an ‘yan sanda sun tura ƙwararrun masu kwance bama-bamai zuwa wuraren da abin ya shafa domin kwashe sauran abubuwan fashewa.

Wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa ya nuna yadda hayaƙi ke tashi daga wani gini da ya lalace gaba ɗaya, yayin da dakarun ceto ke fafutukar neman mutanen da suka ɓace.

Makaman da Iran ta harba sun yi barna a Tel Aviv
Jami'an bada agaji sun taru a wani wuri da makamin Iran ya fada a Tel Aviv na kasar Isra'ila. Hoto: Erik Marmor/Getty Images
Source: Getty Images

Martanin sojojin Isra'ila ga hare-haren Iran

A gefe guda, rundunar sojin Isra'ila (IDF) ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, inda ta bayyana cewa:

“Rundunar sojin sama ta Isra'ila ta kai hari kan wurare fiye da 50 a cikin ƙasar Iran a daren yau, ciki har da wuraren da ake harba makamai.”

Bayanai sun nuna cewa tun bayan ɓallewar wannan yaƙi, Isra'ila ta kai hari kan wurare fiye da 3,000 a cikin ƙasar Iran.

Kalli bidiyon makamin da Iran ta harbar da barnar da ya yi wa Isra'ila a kasa:

An yi ruwan makamai a Tel Aviv

A wani labari, mun ruwaito cewa, Magajin garin Tel Aviv, Ron Huldai, ya tabbatar da cewa wani makami mai linzami da Iran ta harba ya sami wasu gine-gine a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

Harin, wanda ya afku a wani babban yanki dake Arewacin birnin, kuma ya ruguza bangon wani tsohon gini mai hawa uku tare da jawo watsuwar baraguzai a kan titi.

Sojojin Isra'ila sun fitar da gargaɗi har sau bakwai a ranar Talata game da makaman da ake harbowa daga Iran zuwa tsakiya da kudancin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com