Jagorori da Kwamandojin Iran 10 da Aka Kashe tun Bayan Fara Yaki da Amurka, Israila

Jagorori da Kwamandojin Iran 10 da Aka Kashe tun Bayan Fara Yaki da Amurka, Israila

Birnin Tehran, Iran - Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026.

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Hare-haren sun yi sanadiyyar kashe jagoran addini na Iran Ali Khamenei da wasu manyan jami'an siyasa da na soja na kasar.

Isra'ila ta kashe jagorin Iran da dama
Ayatollah Ali Khamenei, Abdolrahim Mousavi da Ali Shamkhani Hoto: NurPhoto, Anadolu
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin manyan jagororin Iran da Amurka da Isra'ila suka kashe tun bayan fara yakin.

An kashe kwamandoji da jagori a Iran

Hare-haren dai sun jawo an hallaka manyan jami'an gwamnati da kwamandojin Iran.

Amma wasu manyan jami'ai sun tsira kuma jamhuriyar Musulunci ta nuna juriya wajen maye gurbin shugabannin da aka kashe cikin sauri, sannan tana ci gaba da yaƙi da Amurka da Isra'ila.

1. Ayatollah Ali Khamenei

Ayatollah Ali Khamenei, wanda shi ne jagoran addini na Iran tun 1989, an kashe shi ne a lokacin farko na yaƙin a ranar 28 ga Fabrairun 2026 a wani hari kan taron manyan jami'ai a Tehran.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Sabani ya shiga tsakanin Trump da Netanyahu, sun yi musayar yawu

Amurka da Isra'ila sun kashe Ali Khamenei
Tsohon jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: @khamenei_ir
Source: Twitter

Harin ya kashe surukarsa, ɗiyarsa, da aƙalla jikansa guda ɗaya, kamar yadda rahoton tashar Aljazeera bayyana.

Ɗansa Mojtaba Khamenei, wanda ba ya cika fitowa fili, ya tsira, kodayake an ba da rahoton cewa ya samu raunuka kuma ya karɓi ragamar shugabancin Iran.

2. Ali Larijani

Shugaban majalisar tsaron kasa, Ali Larijani, ya rasa ransa a wani hari da Isra'ila ta kai domin kashe shi.

Isra'ila ta kashe Larijani a wani hari
Shugaban majalisar tsaron Iran, Ali Larijani Hoto: @alilarijani
Source: Twitter

Kisan Ali Larijani, wanda ba malamin addini ba ne amma jigo ne a gwamnatin Iran na tsawon shekaru da dama, watakila shi ne rashi mafi girma ga jamhuriyar Musulunci bayan mutuwar Ali Khamenei.

An kashe Ali Larijani a ranar 17 ga Maris 2026 a wani harin Isra'ila, wanda aka kai a yankin Tehran kuma ya kashe ’yan uwan sa, jaridar The Guardian ta kawo labarin.

Mako guda kafin nan, ya fito fili a Tehran a wani taron nuna goyon baya ga gwamnati.

Kara karanta wannan

Makaman da Iran ta harba sun gigita Isra'ila, an ji barnar da suka yi

3. Mohammad Pakpour

Babban Kwamandan rundunar IRGC, Mohammed Pakpour, ya rasa ransa a harin da Isra'ila ta kai kan Iran, tashar NDTV ta kawo labarin.

Mohammed Pakpour ya rasa ransa a harin Isra'ila
Mohammed Pakpour wanda Isra'ila ta hallaka Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Pakpur wanda a baya shi ne shugaban dakarun ƙasa na IRGC, ya jagoranci rundunar tun watan Yunin 2025 lokacin da aka kashe tsohon babban kwamanda Hossein Salami a yaƙin kwanaki 12 da Isra'ila ta yi da Iran.

An kashe shi a ranar farko na yaƙin kuma tsohon Ministan cikin gida da tsaro Ahmad Vahidi ya maye gurbinsa.

4. Ali Shamkhani

Mai ba jagoran addini na Iran shawara, Ali Shamkhani, na daga cikin manyan jagororin da Isra'ila ta hallaka.

Ali Shamkhani ya rasa ransa a harin Isra'ila
Ali Shamkhani wanda Isra'ila ta kashe Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Ali Shamkhani wanda jigo ne a dakarun jamhuriyar Musulunci tun shekarun 1980, an kashe shi a wani harin sama a ranar farko ta yaƙin, jaridar Iran International ta kawo rahoton.

5. Esmael Khatib

Ministan leken asiri na Iran, Esmael Khatib, ya rasa ransa a wani harin da Isra'ila ta kai.

Kara karanta wannan

Ana shagulgulan Sallah, ƴan ta'adda sun sace jami'in gwamnatin jihar Kano

Isra'ila ta kashe Esmaeil Khatib
Ministan leken asirin Iran, Esmaeil Khatib Hoto: @QudsNen
Source: Twitter

An kashe Esmael Khatib ne yayin wani harin Isra'ila a Tehran da sanyin safiyar 18 ga Maris 2026, kamar yadda sanarwar da IDF ta sanya a shafinta na X ta nuna.

Ya kasance Ministan leken asiri na Iran tun shekarar 2021, kafin kisan da aka yi masa.

6. Aziz Nasirzadeh

Ministan tsaron Iran, Aziz Nasirzadeh, wanda kwararre ne tun yaƙin Iran da Iraki a shekarun 1980, ya yi aiki a matsayin Ministan tsaro tun 2024.

Israila ta kashe Ministan tsaron Iran, Aziz Nasirzadeh
Ministan tsaron Iran, Aziz Nasirzadeh Hoto: picture alliance
Source: Getty Images

Jaridar Iranwire ta ce Aziz Nasirzadeh ya rasa ransa ne tun harin farko da Isra'ila ta kai kan Iran lokacin da aka fara yakin a karshen watan Fabrairun 2026.

7. Gholamreza Soleimani

Babban kwamandan dakarun Basij, Gholamreza Soleimani, ya shiga sahun kwamandojin Iran da Isra'ila ta kashe.

Isra'ila ta kashe Gholamreza Soleimani
Babban kwamandan dakarun Basij, Gholamreza Soleimani Hoto: Atta Kenare
Source: Getty Images

Gholamreza Soleimani wanda ya jagoranci dakarun Basij, da ke karkashin IRGC an kashe shi a wani harin sama a ranar 17 ga Maris 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila

Rundunar IDF ta tabbatar da kashe Gholamreza Soleimani a shafinta na X a ranar Talata, 17 ga watan Maris 2026.

8. Ali Mohammad Naeini

Isra'ila ta hallaka Mai magana da yawun rundunar IRGC, Ali Mohammad Naeni, yayin wani hari da ta kai.

Isra'ila ta kashe kakakin IRGC
Kakakin rundunar IRGC, Janar Ali Mohammad Naeini, yana jawabi a Tehran. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Rundunar IDF ta Isra'ila ta bayyana a shafinta na X cewa ta kashe Ali Mohammad Naini a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.

9. Mohammad Shirazi

Mohammad Shirazi shi ne shugaba mai kula da bangaren sojoji a ofishin jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Mohammed Shirazi ya rasa ransa a harin Isra'ila
Mohammed Shirazi da wasu jagorori a wurin wani taro a Tehran Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Yana da babban aiki na haɗa kai tsakanin rassa daban-daban na jami'an tsaron Iran a ofishin jagoran addini.

Ya rasa ransa ne yayin harin farko da Isra'ila ta kai a ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026, jaridar Euronews ta kawo labarin.

10. Abdolrahim Mousavi

Abdolrahim Mousavi shi ne shugaban rundunar sojojin Iran kuma an kashe shi a ranar farko na yaƙin, shafin abc.net.au ya kawo labarin.

Israila ta kashe Abdolrahim Mousavi
Shugaban rundunar sojojin Iran, Abdolrahim Mousavi Hoto: Atta Kenare
Source: Getty Images

Ya karɓi muƙaminsa ne a watan Yunin 2025 biyo bayan mutuwar wanda ya gada Mohammad Bagheri a yaƙin kwanaki 12.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Isra'ila ta sake yi wa Iran lahani, ta kashe babban Minista

Iran ta kai hare-hare kan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kaddamar da sababbin hare-haren ramuwar gayya kan kasar Isra'ila.

Rundunar IRGC ta sanar da ƙaddamar da rukuni na 78 na hare-haren ramuwar gayya na "Operation True Promise 4".

IRGC ta bayyana cewa ta kai harin ne kan muhimman wurare a Isra'ila kamar Dimona, Tel Aviv, da Eilat, gami da sansanonin sojojin Amurka da dama a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng