Yayin da Amurka ke Ikirarin Tattaunawa, Iran Ta Yi wa Isra'ila Illa da Makamai Masu Linzami

Yayin da Amurka ke Ikirarin Tattaunawa, Iran Ta Yi wa Isra'ila Illa da Makamai Masu Linzami

  • Kasar Iran ta sake harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila, yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu raunuka a Tel Aviv sanadin harin Iran a birnin wanda ya sake tayar da hankula
  • Rahotanni sun nuna an lalata gine-gine da dama, yayin da Amurka ke kokarin shiga tattaunawa amma Iran ta musanta cewa ana wata sulhu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta sake kai wani sabon hari da makamai masu linzami zuwa Isra’ila a ranar Talata 24 ga watan Maris, 2026.

Harin ya haddasa barna da raunata wasu mutane a birnin Tel Aviv yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila.

Isra'ila ta sake cin karo da mummunan hari daga Iran
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Wannan ya faru ne yayin da ake cikin rashin tabbas kan yiwuwar tattaunawar kawo karshen yakin da ya kwashe kusan makonni uku a yankin Gabas ta Tsakiya, cewar tashar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Sabanin Mojtaba Khamenei, an fadi wanda Trump ke so ya jagoranci Iran

Harin Iran ya illata birnin Tel Aviv a Isra'ila

Hotuna sun nuna yadda tituna suka cika da baraguzai, yayin da wani bangare na gini ya rushe a cibiyar kasuwanci ta Isra’ila.

Masu aikin ceto sun taimaka wa mutane hudu da suka samu raunuka da ba tsanani a wurare daban-daban.

Magajin garin Tel Aviv, Ron Huldai, ya ce wani hari kai tsaye ya lalata wani gini a unguwar masu kudi, inda bidiyo ya nuna yadda bangon ginin ya tsage gaba daya.

Kafofin yada labarai na Iran sun ce jiragen yakin Amurka da Isra’ila sun kai hari kan wuraren gas biyu da kuma bututun mai, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ja da baya daga barazanar kai hari kan makamashi.

Trump ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da wani babban mutum, yana gargadin cewa idan tattaunawar ta gaza cikin kwanaki biyar, za su ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba.

Sai dai shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce babu wata tattaunawa da ake yi, yana zargin Trump da kokarin sarrafa kasuwannin kudi da man fetur.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da bidiyon babban rumbun makamai da ke karkashin kasa

Iran ta sake rikita Isra'ila da manyan hare-hare
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Shugabannin Iran da Pakistan sun tattauna

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya ce ya tattauna da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, yana mai alkawarin taimakon kasarsa wajen samar da zaman lafiya a yankin.

A gefe guda, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Beirut da kudancin Lebanon, inda aka kashe mutane biyu a wani hari, yayin da wasu da dama suka rasa gidajensu.

Wani mazaunin yankin, Abbas Qassem, ya bayyana cewa babu abin da ya rage daga gidansa, yana mai cewa dukiya da komai na da sun lalace gaba daya, cewar Time of Israel.

Hare-haren Isra’ila a Lebanon sun kashe sama da mutane 1,000 tare da tilasta wa fiye da miliyan daya gudun hijira, yayin da adadin wadanda suka mutu a Iran ya haura 3,000 ciki har da fararen hula da dama.

Japan ta magantu kan yakin Iran/Isra'ila

An ji cewa Japan ta ce za ta iya tura sojojinta domin aikin cire nakiyoyi a mashigar Hormuz idan aka cimma tsagaita wuta a yakin Amurka da Isra’ila da Iran.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun razana Netanyahu, ya fito a bidiyo yana neman agaji

Ministan harkokin wajen Japan ya bayyana cewa wannan ra’ayi na hasashe ne kawai, amma zai yiwu idan nakiyoyi sun hana zirga-zirgar jiragen ruwa.

Japan na samun kusan kashi 90 na man fetur ta mashigar Hormuz, lamarin da ya sa tsaro da bude hanyar ya zama muhimmin abu gare ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.