Sabanin Mojtaba Khamenei, an Fadi Wanda Trump zai So Ya Jagoranci Iran

Sabanin Mojtaba Khamenei, an Fadi Wanda Trump zai So Ya Jagoranci Iran

  • A ranar Litinin, Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya tattauna da Iran, lamarin da ya sanya shi janye kai hari kasar
  • Biyo bayan haka, an samu wasu bayanai daga fadar White House da ke nuna cewa Trump na son wani jami'in gwamnati ya jagoranci Iran
  • A halin yanzu dai Mojtaba Khamenei jami'an gwamnatin Iran suka yi wa mubaya'a bayan kashe mahaifinsa a hare-haren da aka kai kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Gwamnatin Donald Trump na duba yiwuwar amfani da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, a matsayin wanda za su yi aiki da shi, har ma da yiwuwar zama jagora a nan gaba.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin Amurka ke nuna sauyi daga matsin lambar soja zuwa neman mafita ta tattaunawa da kasar Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da bidiyon babban rumbun makamai da ke karkashin kasa

Shugaba Donald Trump da Mohammad Bagher Ghalibaf
Shugaba Donald Trump a hagu, Mohammad Bagher Ghalibaf a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Reuters ta wallafa cewa Ghalibaf, mai shekaru 64, wanda ya taba yin barazanar ramuwar gayya ga Amurka da kawayenta, wasu a cikin Fadar White House na kallonsa a matsayin wanda za a iya aiki da shi.

Wane ne zai tattauna da Amurka a Iran?

Wasu jami'an White House sun nuna alamun cewa gwamnatin Trump na fatan Mohammad Bagher Ghalibaf ya zama wanda zai jagoranci tattaunawa da Trump a Iran.

Sai dai har yanzu Fadar White House ba ta yanke shawara kan mutum guda ba, domin tana son gwada mutane da dama domin gano wanda zai amince da yin yarjejeniya.

Wani jami’i a fadar White House ya bayyana Ghalibaf a matsayin “zabi mafi dacewa,” amma ya jaddada cewa ba a yanke hukunci ba tukuna.

Neman wanda za a yi tattaunawa da shi na nuna cewa Amurka na neman hanyar fita daga wannan rikici da ya haddasa tashin farashin mai da girgiza kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Yayin da ake yaki da Iran, jirgin sama ya yi hadari a kasar Amurka

Amurka ta ki yin karin bayani kan batun

Da aka nemi karin bayani, kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce wadannan batutuwa na diflomasiyya ne masu matukar muhimmanci, kuma Amurka ba za ta tattauna su ta kafafen yada labarai ba.

Trump ya kuma nuna cewa yana kokarin tuntubar wasu “mutane masu karfi” a cikin Iran, tare da dakatar da hare-hare kan cibiyoyin makamashi na tsawon kwanaki biyar domin ba da damar tattaunawa.

Mojtaba Khamenei a kasar Iran
Sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da Trump zai so a Amurka

A bangaren tattalin arziki, gwamnatin na son kare muhimman cibiyoyin mai kamar na Kharg, domin tana fatan sabon shugaba zai iya kulla yarjejeniya da Amurka, musamman kan harkar mai.

Sai dai wasu jami’ai sun yi zargin cewa Trump na iya yin wadannan furuci ne domin samun lokaci da kuma rage matsalolin makamashi a kasuwanni, musamman bayan barazanar da ya yi na kai hari idan ba a bude mashigar Hormuz ba.

Politico ta ce gwamnatin Trump na cikin wani mataki na “gwaji,” tana nazarin wanda zai iya zama jagora ko abokin tattaunawa a Iran, yayin da take kokarin kaucewa tsawaita rikicin da kuma nemo mafita ta siyasa.

Kara karanta wannan

Da gaske jiragen Iran sun farmaki ayarin motocin Trump? an samu gaskiyar zance

Bukatun Trump ga kasar Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya fitar da wasu sharuda da ya ce idan Iran ta cika za a samu zaman lafiya.

Ya bayyana cewa yana so Iran ta daina taimakon wasu kungiyoyi da ake fafatawa da su a Gabas ta Tsakiya kamar Hamas da Hizbullah.

Baya ga haka, shugaba Trump ya bukaci Iran ta dakatar da kera makamai masu linzami na tsawon shekara biyar a cikin sharudan da ya fitar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng