Ana Wata ga Wata: Iran Ta Yi Martani kan Ikirarin Trump Na Fara Tattauna kan Yakin da Ake Yi

Ana Wata ga Wata: Iran Ta Yi Martani kan Ikirarin Trump Na Fara Tattauna kan Yakin da Ake Yi

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fito ya ikirarin cewa ya fara tattaunawa da Iran kan yakin da ake yi
  • A cewar Trump, tattaunawar ta fara haifar da sakamako mai kyau wanda hakan ya sanya ya ba da umarnin dakatar da shirin kai hare-hare kan tashoshin lantarkin Iran
  • Sai dai, an ji daga bakin wani jami'in Iran kan ko ana tattaunawa tsakanin Donald Trump da mahukuntan kasar

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Wani babban saɓani ya fito fili tsakanin Washington da Tehran game da yanayin tuntuɓar juna ta hanyar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya tattauna da Iran kuma tattaunawar ta samar da sakamako mai kyau kuma za a ci gaba da yin ta.

Iran ta yi wa Trump martani kan tattaunawa
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kasar Iran ta musanta cewa an yi tattaunawa tsakanin mahukunta a kasar da Donald Trump.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya janye kai mummunan hari Iran, ya fadi dalilan daukar matakin

Trump ya ce yana tattaunawa da Iran

A ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026, Trump ya bayyana cewa ƙasashen biyu sun yi tattaunawa mai kyau da amfani sosai a cikin kwanaki biyun da suka gabata, da nufin cimma mafita kan rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban na Amurka ya ce ya ba da umarnin dakatar da barazanar hare-haren da ya yi niyyar kaiwa kan tashoshin samar da lantarki da makamashin Iran sakamakon tattaunawar, wanda hakan ya nuna kamar an samu gagarumar nasara ta diflomasiyya.

Wane martani Iran ta yi?

Sai dai, Iran ta hanzarta ƙaryata wannan bayani, inda wani babban jami'in tsaron Iran ya yi watsi da iƙirarin Trump baki ɗaya.

A cewar jami'in Trump ya janye tayin tattaunawar ne saboda barazanar soja mai ƙarfi da Iran ta yi da kuma ƙaruwar matsin lamba na kuɗi a kan Amurka da ƙasashen Yamma.

Jami’in ya fito fili wajen yin watsi da ra’ayin cewa ana gudanar da kowace irin tattaunawa, tashar Aljazeera ta dauko labarin.

Kara karanta wannan

Trump ya gaji da jira, ya ba Iran wa'adin awa 48 ko ya yi mata illa mai muni

Trump ya yi ikirarin fara tattaunawa da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

Iran na ci gaba da dagewa kan matsayarta

Tun farkon fara yakin Amurka da Isra'ila kan Iran, saƙonni daga masu shiga tsakani zuwa Tehran ana tarbar su ne da matsayi mai ƙarfi, Iran za ta ci gaba da kare kanta har sai an cimma nasarar dakatar da maƙiya.

"Ba a gudanar da tattaunawa, kuma yaƙin wasa da tunani ba zai dawo da Mashigar Hormuz ko daidaita kasuwannin makamashi ba."

- Wani jami'in Iran

Jami'in ya ƙara da cewa wa'adin kwanaki biyar na Trump ya nuna ci gaba da shirye-shiryen ƙarin hare-hare, shirye-shiryen da Iran ta ce za ta tarbe su da cikakken martanin kariya.

Batun kudin yaki da Iran

A wani labarin kuma kun ji cewa Ministan kudin Amurka, Scott Bessent, ya yi tsokaci kan yakin da ake yi da Iran.

Scott Bessent ya yi iƙirarin cewa Washington za ta iya ɗaukar nauyin yaƙi da Iran cikin sauƙi kuma ba za ta buƙaci ƙara haraji don yin hakan ba.

Ministan kudin ya bayyana cewa Amurka na da isassun kudin da za ta ci gaba da daukar nauyin yakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng