Iran Ta Fitar da Bidiyon Babban Rumbun Makamai da ke karkashin Kasa
- Gwamnatin Iran ta fitar da wani bidiyo da ta nuna manyan makamai da ta mallaka a wani gini a karkashin kasa yayin da take yaki da Isra'ila da Amurka
- A cikin bidiyon, Legit Hausa ta hango wasu manyan motoci da ake amfani da wasu wajen harba makamai masu linzami zuwa waje mai nisa
- A gefe guda kuma, mai magana da yawun wani rukuni na sojojin Iran, Ebrahim Zolfaghari ya yi wa Donald Trump martani mai cike da tsokana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Kasar Iran ta fitar da wani bidiyo da ke nuna cewa a shirye ta ke wajen cigaba da fafatawa da kasashen Amurka da Isra'ila a yakin da suke.
A wani bidiyo da kasar ta wallafa, ta nuna tarin kayan fada jim kadan bayan Donald Trump ya yi barazanar kai mata hari kan na'urorin lantarki.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta wallafa bidiyon da kasar ta fitar tare da yin karin bayani a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, 23 a watan Maris, 2026.
Makaman da Iran ta nuna a bidiyo
Wani bidiyo da gidan talabijin na gwamnatin Iran ya fitar ya nuna jerin makamai masu linzami da aka adana a wani rumbun karkashin kasa.
Gidan talabijin din ya bayyana wannan tarin makamai a matsayin “kadan daga cikin abin da suke da shi,” yana nufin cewa akwai karin makamai da ba a nunawa duniya ba.
Iran ta nuna tarin makaman ne yayin da shugaban Amurka, Donald Trump ya sha alwashin cewa ya gama lalata makaman da take da shi.
A bidiyon, Iran ta nuna manyan motocin da ake harba makamai, tarin makamai masu linzami a wani waje mai kama da bene a karkashin kasa.
Ga bidiyon rumbun makaman Iran a kasa:
Iran ta yi wa Trump shagube
A wani bangare kuma, kakakin rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya, Ebrahim Zolfaghari, ya yi wa shugaban Amurka, Donald Trump, wani irin martani mai cike da tsokana.
Ebrahim Zolfaghari ya yi wa Trump martani ne yayin da wa’adin da Amurka ta bayar na bude mashigin Hormuz ke daf da karewa.
Jaridar Times of India ta wallafa cewa Zolfaghari ya ce:
“Kai Trump, an gama da kai ! Ka saba jin wannan kalma. Na gode da kulawarka,”

Source: Getty Images
Iran ta kuma bayyana cewa za ta kai hare-haren ramuwar gayya masu tsanani idan Amurka ta aiwatar da barazanar da ta yi na kai hari kan cibiyoyin makamashin kasar saboda ci gaba da toshe mashigar Hormuz.
NATO za ta tunkari kasar Iran
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar NATO ta yi magana game da shirin da take yi domin tunkarar Iran kan toshe mashigar Hormuz.
Shugaban NATO ya sanar da cewa kasashe 22 sun amince wajen hada kai su tabbatar da an bude mashigar ga kasashen duniya.
Tun a baya, Shugaban Amurka, Donald Trump ya caccaki kasashen NATO kan kin taimaka masa wajen tilasta Iran bude mashigar Hormuz.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


