A Karshe, Trump Ya Fadi Abin da Iran za Ta Yi Masa a Samu Zaman Lafiya
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana abin da ya ke bukata daga kasar Iran domin samun zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu
- Trump ya yi magana ne yayin da aka shiga mako na uku ana gwabza yaki da Iran bayan jerin hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai Tehran
- Masu sharhi sun bayyana cewa ba lallai Iran ta saurari bukatar Trump ba lura da cewa ta shafi shirin ta na mallakar makamai masu linzami
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Donald Trump ya fara magana game da neman shiryawa da Iran bayan shafe sama da kwana 20 ana gwabza yaki.
Trump ya mika bukata ga gwamnatin Iran game da mallakar makamai masu linzami, inda ya ce hakan zai sanya samun zaman lafiya a tsakaninsu.

Source: Getty Images
Rahoton jaridar Telegraph da ke Birtaniya ya nuna cewa Trump ya yi maganar ne duk da cewa a baya ya ce ba shi bukatar tattaunawa da Iran saboda ya gama da kasar.
Bukatar Donald Trump ga kasar Iran
Donald Trump ya bukaci Iran ta dakatar da shirinta na makamai masu linzami na tsawon shekaru biyar a matsayin sharadin samun zaman lafiya.
Wannan na daga cikin sharudda guda shida da shugaban Amurka ke son Tehran ta amince da su, lamarin da ke nuna cewa matsayar Amurka da Iran na kara nisa da juna.
Fadar White House ta kuma ki amincewa da kiran tsagaita wuta, yayin da Iran ke jaddada cewa ba za a fara tattaunawa ba sai an dakatar da fada.
Wasu daga cikin bukatun da Trump ya nema sun hada da daina shirin mallakar nukiliya, dakatar da taimakawa kungiyoyi kamar Hamas da Hisbullah.
Haka zalika shugaban Amurka ya bukaci Iran da takaita shirin mallakar makamai masu hadari da za su iya wuce kima a Gabas ta Tsakiya.
Iran da kasar Amurka na takun saka
Bayan fiye da mako biyu da fara rikicin, bangarorin biyu na bayar da sakonni masu cin karo, inda a gefe guda suke nuna yiwuwar diflomasiyya, amma a gefe guda kuma suna ci gaba da kalaman yaki.
Trump ya bayyana karara cewa ba ya goyon bayan dakatar da yaki nan take, yana mai cewa dole ne a ci gaba da matsin lamba na soja domin tilasta Iran ta amince da wasu sharuda.

Source: Getty Images
Iran International ta wallafa cewa ya ce:
“Ba na son tsagaita wuta… ba ka tsagaita wuta lokacin da ka ke murkushe abokin fada,”
A farko farkon yakin, shugaban Amurka ya nuna cewa yaki da Iran zai iya karewa ne kawai idan shugabancin kasar ya rushe baki daya.
Isra'ila ta nemi agajin kasashe
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin kasar Isra'ila ta bukaci kasashen duniya su hada kai da ita wajen yaki da kasar Iran a Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa Benjamin Netanyahu ne ya yi kiran yayin da ya ziyarci birnin Arad da Iran ta yi wa luguden wuta a ranar Lahadi.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa Iran na da makaman da za su iya isa har kasashen Turai, amma Birtaniya ta karyata hakan nan take.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


