An Rufe Makarantu: Halin da Ake Ciki a Isra'ila bayan Harin Iran, an Hana Taro

An Rufe Makarantu: Halin da Ake Ciki a Isra'ila bayan Harin Iran, an Hana Taro

  • Kasar Isra’ila ta ayyana dokar ta-baci bayan Iran ta harba makamai masu linzami wanda ya jawo hana yawan taruwar mutane
  • An kwashe marasa lafiya zuwa karkashin kasa a asibitoci yayin da aka kira sojojin ajiyar gaggawa domin kare iyakoki daga hare-haren makamai
  • Duk da barazanar, wasu mazauna Tel Aviv sun nuna kwarin gwiwa da tsarin kariya na iska, suna goyon bayan matakin soja na Isra'ila

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tel Aviv, Israel - Isra’ila ta ayyana dokar ta-baci a fadin kasar bayan Iran ta harba makamai zuwa kasar a matsayin martani ga harin hadin gwiwa da Amurka ta kai.

An rufe makarantu, wuraren aiki da kuma dakatar da tarukan jama’a, yayin da aka fara daukar matakan tsaro masu tsauri domin kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

Matakan da Isra'ila ta dauka bayan harin Iran
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Ministan tsaro, Israel Katz, ya gargadi ‘yan kasa kan yiwuwar karin hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki a sassa daban-daban na kasar, cewar Al Jazeera.

An tsaurara tsaro a kasar Isra'ila

An kira dubban sojojin ajiyar gaggawa domin karfafa tsaron kan iyakoki, yayin da ‘yan sanda suka bukaci jama’a su guji tafiye-tafiye marasa muhimmanci domin saukaka ayyukan gaggawa.

A Tel Aviv, wasu mazauna sun fita bakin teku duk da halin da ake ciki, suna nuna amincewa da tsarin kariya na iska da ke kare biranen daga hare-hare.

Wata mata mai suna Shira Dorany ta ce:

"Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan yanayi, bana son jira abin da zai zo gaba.”

Tsarin gargadin kasa ya rika umartar mazauna su shiga mafaka yayin da ake dakile makaman da aka harba, tare da samun rahotannin karancin barna da asarar rayuka.

A asibitin Sheba da ke kusa da Tel Aviv, an kwashe marasa lafiya da sassan aiki gaba daya zuwa wuraren kariya da ke karkashin kasa domin tsira.

Kara karanta wannan

Lamari ya kwabe: Saudiyya ta kori sojoji, jami'an diflomasiyyar Iran daga kasar

Harin Iran ya rikita kasar Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Harin Iran: Matakan da Isra'ila ta dauka

Shugaban asibitin, Itai Pessach, ya bayyana cewa sun shiga yanayin shiri na musamman domin fuskantar duk wani hari da zai iya biyo baya.

Isra’ila ta kuma rufe sararin samaniya ga jiragen farar hula, amma ta bar iyakokin kasa da Egypt da Jordan a bude, cewar The Jerusalem Post.

A Jerusalem, jama’a sun rika sayen abinci da cire kudi yayin da ake jin karar fashewar makamai a sararin sama sakamakon dakile hare-hare.

Ofishin jakadancin Amurka ya bukaci ma’aikatansa su zauna a mafaka, yana mai tunatar da su umarnin da aka bayar tun farko kan yiwuwar barin kasar idan suka so.

Wannan rikici ya biyo bayan yakin sama na kwanaki 12 da aka yi a bara tsakanin Isra’ila da Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

An karyata nada sabon Firayim ministan Isra'ila

An ji cewa wasu sakonni a kafofin sadarwa sun yi ta yada cewa wai an zabi sabon Firayim ministan Isra'ila domin maye gurbin Benjamin Netanyahu.

Kara karanta wannan

Trump zai sauya salon yaki da Iran, sojojin Amurka 2,500 sun nufi Gabas ta Tsakiya

Sakon ya yi ikirarin cewa Yariv Levin ya zama Firayim ministan rikon kwarya a madadin Benjamin Netanyahu, wanda aka yi binciken kwa-kwaf.

Babu wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da saukar Benjamin Netanyahu ko nadin Yariv Levin, lamarin dai jita-jita ne daga shafukan sadarwa kadai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com