An Zo Wajen: Amurka Ta Yi Magana kan Ci Gaba da Daukar Nauyin Yaki da Iran
- Ministan kudi na Amurka, Scott Bessent, ya yi magana kan yakin da kasarsa ke yi da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
- Scott Bessent ya tabo batun kudaden da ake bukata domin ci gaba da daukar nauyin yakin da ake yi da Iran
- Ministan ya kuma yi watsi da batun yiwuwar kara haraji domin samun kudaden da za a ci gaba da yin yakin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Birnin Washington, Amurka - Ministan kudin Amurka, Scott Bessent, ya yi magana kan samo kudaden yakin da Amurka ke yi da Iran.
Scott Bessent ya yi iƙirarin cewa Washington za ta iya ɗaukar nauyin yaƙi da Iran cikin sauƙi kuma ba za ta buƙaci ƙara haraji don yin hakan ba.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce Scott Bessent ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a shirin NBC News mai suna Meet the Press.
Shin Amurka na da kudin yaki da Iran
Scott Bessent ya bayyana cewa buƙatar ƙarin kasafi da ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ke nema,wanda aka ruwaito ya kai $200bn, zai kasance ne don ƙarfafa ayyukan soja na nan gaba.
Ministan ya bayyana cewa Amurka na da isassun kudin da za ta ci gaba da daukar nauyin yakin.
"Muna da isassun kuɗi da za mu ɗauki nauyin wannan yaƙin. Shugaba Trump ya gina rundunar sojoji, kamar yadda ya yi a wa'adinsa na farko, kuma kamar yadda yake yi yanzu a wa'adinsa na biyu.
"Kuma yana son tabbatar da cewa rundunar tana da isassun kayan aiki a nan gaba."
- Scott Bessent
Ana cece-kuce kan kudin da Amurka ke nema
Wannan buƙatar ƙarin kuɗi tana fuskantar adawa mai tsanani a majalisa, inda 'yan jam'iyyar Democrat da ma wasu daga jam'iyyar Republican ke nuna ayar tambaya kan buƙatar, bayan an ware manyan maƙudan kuɗaɗen tsaro a shekarar da ta gabata.
Jaridar The Economic Times Bessent ya kare wannan buƙatar ba tare da tabbatar da adadin ba.
Har yanzu Shugaba Donald Trump bai aika da buƙatar ga majalisar dattawa da ta wakilai don amincewa da kuɗin ba, kuma gwamnatinsa ta bayyana sarai cewa adadin na iya canzawa.
Scott Bessent ya yi watsi da batun yiwuwar ƙara haraji inda ya kira hakan a matsayin “abin dariya,” sannan ya ce hakan “sam ba ya” cikin tsari.
Alamun farko na nuna cewa yaƙin zai kasance mafi tsada ga Amurka tun bayan dogayen rikice-rikicen Iraƙi da Afganistan.
Jami’an gwamnati sun shaida wa ’yan majalisa cewa kwanaki shida na farko na yaƙin Iran sun ci fiye da 11.

Source: Facebook
Batun dage takunkumi kan Iran da Rasha
Bessent ya kuma kare matakan da gwamnatin Trump ta ɗauka a kwanakin nan na ɗage takunkumi kan man fetur na Iran da Rasha.
Yin hakan, in ji shi, zai ba sauran ƙasashe baya ga China ciki har da Japan da Koriya ta Kudu damar siyan man, yayin da hakan zai hana farashin man tashi zuwa dala 150 a kowace ganga, sannan zai rage yawan kuɗaɗen shigar da Iran da Rasha za su samu.
Ana tsoron shirin Amurka
Kwamred Sa'idu Bello, fitaccen mai sharhi game da harkokin Gabas ta Tsakiya ya shaida wa Legit Hausa cewa akwai tsoron Amurka ta kai harin makamin nukiliya Iran.
Ya ce:
"Kwanaki Donald Trump ya ce Amurka na duba yiwuwar kawo ƙarshen yaƙi da Iran. Akwai wadanda ke tsoron ko za a kai harin makamin nukiliya ne."
Sai dai, Sadiq Madabo, ya taba shaida wa Legit Hausa cewa yanzu an ga sauyi sosai a yadda Iran ta ke kai hare-hare, sabanin shekarun baya.
Sadiq, wanda dan Najeriya ne mazaunin Kuwait, bayyana cewa, su da suke a Gabas ta Tsakiya, sun gaskata karin karfin Iran.
"A yanzu na ga hakikanin karfin Iran, domin kan ka ce me, sun kai hare-hare a kasashe bakwai na Larabawa. Amma ina rokon Allah ya takaita, don idan ya wuce haka, to wasu kasashe za su iya shiga."
- Sadiq Madabo.
Iran ta yi wa Trump martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta yi martani mai zafi kan barazanar da Donald Trump, ya yi ta lalata tashoshin samar da wutar lantarki na kasar.
Babbar rundunar gudanarwar Iran ta yi gargaɗin rufe mashigar Hormuz baki ɗaya idan aka kai hari kan wuraren samar da wutar lantarki na kasar.
Kakakin rundunar ya nanata cewa dakarun sojoji a shirye suke su lalata dukkan muradun tattalin arzikin Amurka a yankin Yammacin Asiya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng



