Iran Ta Ki Tsorata da Barazanar Trump, Ta Fadi Matakan da Ta Shirya Dauka
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayin da ake ci gaba da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya
- Donald Trump ya yi barazanar lalata tashoshin samar da wutar lantarki na Iran idan har ba ta bude mashigar Hormuz ba
- Sai dai, Iran ta fito ta yi martani mai zafi kan barazanar da Trump ya yi, inda ta bayyana abin da za ta yi idan har ya cika alwashin da ya dauka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Birnin Tehran, Iran - Babbar rundunar gudanarwar Iran ta yi martani kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi.
Babbar rundunar ta yi gargaɗin rufe mashigar Hormuz baki ɗaya idan aka kai hari kan wuraren samar da wutar lantarki na Iran.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta ce kakakin babban hedkwatar Khatam al-Anbiya, Laftanal Kanar Ebrahim Zolfaqari, ya fitar da wannan gargaɗin ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris 2026.
Wane martani Iran ta yi wa Trump?
Kakakin ya yi gargadin ne a matsayin martani ga barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na kai hari kan tashoshin wutar lantarkin Iran idan ƙasar ba ta "buɗe Mashigar Hormuz baki ɗaya ba, ba tare da barazana ba, nan da sa'o'i 48."
Zolfaqari ya ce Iran za ta ɗauki matakan "hukunci na gaggawa" idan aka kai hari kan wuraren samar da man fetur da makamashi na ƙasar.
“Mun sha bayyana cewa Mashigar Hormuz a rufe take ga makiya kawai da kuma wucewar da ke da cutarwa a gare mu, kuma har yanzu ba a rufe ta baki ɗaya ba, tana ƙarƙashin ikonmu.”
"Ana ci gaba da zirga-zirgar da ba ta da cutarwa a ƙarƙashin takamaiman ƙa'idoji waɗanda ke tabbatar da tsaro da muradunmu."
- Laftanar Kanal Ebrahim Zolfaghari
Wane mataki Iran za ta dauka?
Kakakin ya jaddada cewa idan aka aiwatar da barazanar kan tashoshin wutar lantarkin Iran, kasar za ta rufe Mashigar Hormuz baki ɗaya kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an sake gyara wuraren da aka lalata.
Ya ce za a nufi dukkan tashoshin samar da wutar lantarki na Isra'ila, wuraren samar da makamashi, da tsarin fasahar yaɗa labarai da sadarwa (ICT),.tashar Aljazeera ta kawo labarin.
A cewarsa Iran kuma za ta rugurguza dukkan makamantan kamfanoni masu hannun jarin Amurka a yankin.
Zolfaqari ya ci gaba da gargaɗin cewa tashoshin wutar lantarki a ƙasashen yankin da ke karɓar bakuncin sansanonin Amurka su ma za a ɗauke su a matsayin halatattun wuraren kai hari ga Iran.

Source: Facebook
Iran ta bayyana shirin da take da shi
Kakakin ya sake nanata cewa dakarun sojoji a shirye suke su lalata dukkan muradun tattalin arzikin Amurka a yankin Yammacin Asiya baki ɗaya.

Kara karanta wannan
An zo wajen: Trump ya yi magana kan tsagaita wuta a yakin Amurka, Isra'ila da Iran
Ya sake tabbatar da cewa Iran ba ita ce ta fara yaƙin ba kuma ba za ta ƙara rura wutar rikicin ba, amma idan maƙiyi ya yi barna ga tashoshin wutar lantarkin ƙasar, Iran ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare muradunta.
Ya yi gargaɗin cewa matakan "ba kakkautawa" na lalata wuraren makiya, za su fara idan aka kai hari kan tashoshin wutar lantarkin Iran.
“Babu abin da zai iya hana mu ci gaba da gudanar da aikinmu na rugurguza wuraren makamashi da man fetur da masana’antun Amurka da kawayenta a yankin."
- Laftanar Kanal Ebrahim Zolfaqari
Iran ta farmaki jirgin yakin Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta yi iƙirarin cewa dakarunta sun harbi wani jirgin saman yaƙin Isra'ila samfurin F-16.
IRGC ta bayyana cewa dakarunta sun harbi jirgin saman yakin ne lokacin da ya ke shawagi a sararin samaniyar Iran.
Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ya fuskanci harbi daga ƙasa a sararin samaniyar Iran.
Asali: Legit.ng

