Japan Ta Yunkuro, Ta Fadi Mataki 1 da Za Ta Iya Dauka kan Yakin Amurka da Iran
- Kasar Japan ta ce za ta iya tura sojojinta domin aikin cire nakiyoyi a mashigar Hormuz idan aka cimma tsagaita wuta a yakin Amurka da Isra’ila da Iran
- Ministan harkokin wajen Japan ya bayyana cewa wannan ra’ayi na hasashe ne kawai, amma zai yiwu idan nakiyoyi sun hana zirga-zirgar jiragen ruwa
- Japan na samun kusan kashi 90 na man fetur ta mashigar Hormuz, lamarin da ya sa tsaro da bude hanyar ya zama muhimmin abu gare ta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Japan - Kasar Japan ta yi magana kan yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.
Japan ta ce za ta iya duba yiwuwar tura rundunar tsaron kanta domin aikin cire nakiyoyi a mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Iran/Isra'ila: Matakin da Japan za ta dauka
Rahoton Reuters ya ce Japan ta za ta dauki matakin idan aka cimma cikakken tsagaita wuta a rikicin Amurka da Isra’ila da Iran.
Ministan harkokin wajen kasar, Toshimitsu Motegi, ya bayyana hakan yayin wata hira, inda ya ce wannan magana ta kasance hasashe ne kawai, amma akwai yiwuwar hakan.
Ya kara da cewa idan aka samu tsagaita wuta kuma nakiyoyin ruwa suna hana zirga-zirga, to zai dace a yi la’akari da aikin cire su.
Duk da haka, dokokin Japan na bayan yakin duniya sun takaita ayyukan soja, sai dai dokar tsaro ta 2015 ta ba da damar tura sojoji idan barazana ta shafi rayuwar kasar.
Motegi ya ce Japan ba ta da shirin gaggawa na neman hanyoyin wucewa ga jiragen ruwanta da suka makale, amma ya jaddada muhimmancin bude mashigar ga kowa.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta rufe mashigar Hormuz a lokacin rikicin, wanda yanzu ya shiga mako na hudu, lamarin da ya janyo tashin farashin mai a duniya.

Source: Getty Images
Yadda Japan ta dogara da man Hormuz
Japan na dogaro da kusan kashi 90 na man fetur daga wannan mashiga, wanda ya sa take fuskantar matsin lamba wajen kare bukatun makamashinta.
A gefe guda, ministan harkokin wajen Iran ya ce sun tattauna da Japan kan yiwuwar bai wa jiragen da ke da alaka da Japan damar wucewa.
Shugaban Amurka ya bukaci Japan da sauran kawaye su kara taka rawa wajen bude mashigar, amma har yanzu ba a samu cikakken amincewa ba.
Firayim ministar Japan ta bayyana cewa ta yi wa shugaban Amurka bayani kan irin taimakon da dokokin kasar su ke ba ta damar bayarwa a wannan lamari.
Iran ta Yi martani ga kawayen Amurka
An ji cewa kasar Iran ta yi martani ga kasashe a duniya bayan barazanar Amurka game da rufe mashigar Hormuz da aka yi.
Iran ta ce mashigan Hormuz a bude yake ga jiragen ruwa, sai dai wadanda ke da alaka da abokan gabanta, yayin da rikici ke kara tsananta.
Jami’in Iran Ali Mousavi ya bayyana cewa jiragen da ba na makiya ba za su iya wucewa idan sun hada kai da Tehran wajen tsaro da aminci.
Asali: Legit.ng

