Abin da Muka Sani kan Jita Jitar Naɗa Sabon Firayim Ministan Isra'ila madadin Netanyahu

Abin da Muka Sani kan Jita Jitar Naɗa Sabon Firayim Ministan Isra'ila madadin Netanyahu

  • Wasu sakonni a kafofin sadarwa sun yi ta yada cewa wai an zabi sabon Firayim ministan Isra'ila domin maye gurbin Benjamin Netanyahu
  • Sakon ya yi ikirarin cewa Yariv Levin ya zama Firayim ministan rikon kwarya a madadin Benjamin Netanyahu, wanda aka yi binciken kwa-kwaf
  • Babu wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da saukar Benjamin Netanyahu ko nadin Yariv Levin, lamarin dai jita-jita ne daga shafukan sadarwa kadai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - A kwanakin nan aka yi ta yada rahoton cewa wai an nada sabon Firayim ministan Isra'ila domin maye gurbin Benjamin Netanyahu.

Wani sako da ya bazu a kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa an nada Yariv Levin a matsayin Firayim ministan rikon kwarya na Isra’ila, domin maye gurbin Netanyahu.

Kara karanta wannan

Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

Bau gaskiya kan maye gurbin Netanyahu da sabon Firayim minista
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Yariv Levin. Hoto: Jack GUEZ / GIL COHEN-MAGEN/POOL/ AFP.
Source: Getty Images

Sakon ya bayyana cewa an yi wannan canjin ne a wani lokaci mai muhimmanci, inda kasar ke fuskantar matsalolin tsaro da kuma muhawara kan dokoki da za su iya sauya makomar kasar, cewar Newsweek.

Binciken kwa-kwaf kan zargin sauya Benjamin Netanyahu

Sai dai binciken gaskiya ya nuna cewa wannan ikirari ba shi da tushe, domin babu wata sanarwa ta hukuma da ta nuna cewa Benjamin Netanyahu ya sauka daga mukaminsa.

Haka kuma, babu wata hukuma da ta tabbatar da cewa Yariv Levin ya karbi ragamar mulki, inda aka gano cewa asalin labarin ya fito ne daga wani shafin Headlines360 na Facebook.

Rahoton ya kara da cewa, an samu yaduwar wani bidiyo da ke nuna Netanyahu da yatsu shida a hannu, wanda wasu suka ce alamar kirkirar na’urar AI ce, cewar rahoton Meyka.

Sai dai bincike ya nuna cewa bidiyon ba gaskiya ba ne, domin an tabbatar cewa hannunsa yana da yatsu biyar kamar yadda aka saba, don haka jita-jitar karya ce.

Kara karanta wannan

Da gaske jiragen Iran sun farmaki ayarin motocin Trump? an samu gaskiyar zance

Ofishin Firayim ministan ya bayyana cewa Benjamin Netanyahu yana cikin koshin lafiya, kuma labaran da ke cewa ya mutu ko ya sauka daga mulki duk karya ne.

Har yanzu Netanyahu ne Firayim ministan Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila da ke yaki da Iran. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Mukaman da Levin ya rike a kasar Isra'ila

Yariv Levin dai yana rike da mukamin mataimakin Firayim minista, tare da wasu mukamai kamar ministan shari’a da harkokin addini a karkashin jam’iyyar Likud.

A karshe, an tabbatar da cewa duk ikirarin da ke cewa an nada shi Firayim ministan rikon kwarya ba gaskiya bane, kuma jita-jita ce kawai da ta samo asali daga kafafen sada zumunta.

An ƙaryata rahoton hari kan motocin Trump

A baya, an ji cewa wasu sun yi ta yada wasu rahotanni wai cewa jirage marasa matuki na kasar Iran sun farmki ayarin motocin Shugaba Donald Trump na Amurka.

Lamarin ya jawo muhawara amma wani bincike ya yi karin haske kan ikirarin da ake yi yayin da yaki ke ci gaba da gudana wanda ya jawo rasa asarar rayuka da dama a yankin.

Hotunan da aka yada tare da labarin an gano cewa kirkirarru ne ko an sauya su, wasu ma daga wata ziyara ce ta daban wanda ba ta da alaka da abin da ake yadawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.