Ana tsaka da Yakin Iran da Isra’ia, Jirgin Sama Ya Yi Hatsari, Sojoji Sun Mutu

Ana tsaka da Yakin Iran da Isra’ia, Jirgin Sama Ya Yi Hatsari, Sojoji Sun Mutu

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa akalla mutane shida sun mutu bayan wani jirgin helikwafta na sojan Qatar ya fadi sakamakon matsalar fasaha
  • Hukumomi sun ce mutum guda har yanzu ba a san inda ya ke ba, yayin da ake ci gaba da aikin nema a cikin ruwan kasar
  • Gwamnati ta ce hatsarin bai da alaka da wani hari ba, duk da tashin hankali da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya dalilin yaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Qatar - Wasu jami'an sojoji daga kasar Qatar sun gamu da tsautsayi bayan jirgin saman da suke ciki ya yi mummunan hatsari.

Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu bayan wani jirgin helikwafta na rundunar sojin Qatar ya fadi a cikin ruwan kasar sakamakon matsalar fasaha.

Sojojin Qatar sun mutu a hatsarin jirgi
Wasu daga cikin jragen saman Qatar a Gabas ta Tsakiya. Hoto: Arab News.
Source: UGC

Ma’aikatar cikin gida ta kasar ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike tare da aikin ceto domin gano mutumin da ya bace, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Sokoto bayan Turji ya yi barazanar tayar da kauye guda

Yadda yakin Gabas ta Tsakiya ke cinye rayuka

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila da take samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.

Yankin Gabas ta Tsakiya ya shiga mummunan yanayin ne bayan garin farko a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Harin ya yi sanadiyar mutuwar marigayi tsohon jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei a birnin Tehran.

Jirgin Qatar ya yi hatsari a Gabas ta Tsakiya
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Yawan mutanen da suka mutu a jirgin Qatar

Rahotanni sun ce mutane bakwai ne ke cikin jirgin lokacin da hatsarin ya faru, inda jami’an tsaro ke ci gaba da neman mutum guda da har yanzu ba a gano shi ba.

Tun da farko, ma’aikatar tsaron Qatar ta bayyana cewa jirgin ya samu matsalar fasaha ne yayin wani aiki na yau da kullum kafin ya fadi.

Hukumomi ba su bayyana karin bayani kan musabbabin hatsarin ba ko sunayen wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Da gaske jiragen Iran sun farmaki ayarin motocin Trump? an samu gaskiyar zance

Babu alakar hatsarin da yakin Iran da Isra'ila

Sai dai an jaddada cewa babu wata alama da ke nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon wani hari daga waje.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali a yankin, bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran tun daga ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Ana ci gaba da tattara bayanai kan lamarin domin tabbatar da dakile faruwar hakan a nan gaba da kuma kare rayukan sojoji, cewar rahoton Reuters.

Jirgin saman Amurka ya rikito daga sama

A wani labarin, an ji cewa rundunar sojin Amurka ta tabbatar da bacewar jirgin dakon manta a yammacin Iraki yayin da ake gudanar da farmakin Epic Fury kan kasar Iran.

Jami'an soji sun bayyana cewa ba wai harin makiya ne ya jawo bacewar jirgin ba, kuma ana cigaba da kokarin neman mutanen da ke cikinsa.

Wannan ne jirgi na hudu da Amurka ta rasa a yakin Gabas ta Tsakiya bayan an kakkabo jiragen F-15 guda uku a kasar Kuwait bisa kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.