Lamari Ya Kwabe: Saudiyya Ta Kori Sojoji, Jami’an Diflomasiyyar Iran daga Kasar

Lamari Ya Kwabe: Saudiyya Ta Kori Sojoji, Jami’an Diflomasiyyar Iran daga Kasar

  • Kasar Saudiyya ta sallami wasu daga cikin jami’an diflomasiyyar Iran biyar tare da ba su awa 24 su fice daga kasar
  • Matakin ya biyo bayan hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai da ake zargin Iran na kai wa cibiyoyin mai da fararen hula
  • Rikicin Amurka, Isra'ila da Iran ya kara dagula yankin tare da tasiri kan kasuwar makamashi ta duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudi Arabia - Gwamnatin kasar saudiyya ta umarci jami’an diflomasiyyar Iran da su fice daga kasar nan take.

Sauran da aka kora sun hada da jami’in soja da wasu ma’aikata hudu su bar kasar cikin awa 24, bayan zargin kai hare-hare akai-akai.

Saudiyya ta kori jami'an soja da wasu jami'an diflomasiyyar Iran
Dan Sarkin Saudiyya, Muhammad Bn Salman. Hoto: Inside the Haramain.
Source: Twitter

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana cewa ta ayyana jami’an a matsayin “wadanda ba a maraba da su,” cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Trump ya gaji da jira, ya ba Iran wa'adin awa 48 ko ya yi mata illa mai muni

Dalilin Saudiyya na sallamar wasu yan Iran

Duka wannan mataki na zuwa ne sakamakon hare-haren da take dangantawa da Iran a cikin kasar.

Wannan mataki ya zo ne yayin da rikici tsakanin amurka da isra’ila da Iran ke kara tsananta, inda ake zargin Tehran da kai hare-hare kan kasashen yankin da ke dauke da sansanonin sojojin Amurka.

Tun bayan fara yakin, saudiyya ta ce ta fuskanci daruruwan hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki, kodayake mafi yawansu an dakile su kafin su yi barna.

Rahotanni sun nuna cewa cibiyoyin makamashi a gabashin saudiyya da babban birnin Riyadh sun sha fama da hare-hare, ciki har da harin jirage marasa matuki da suka taba kai wa ofishin jakadancin amurka.

Haka kuma, an samu cikas a tashar fitar da mai ta Yanbu bayan harin jirgi maras matuki da ya fado kusa da matatar mai ta Aramco-Exxon.

Tashar Yanbu ita ce muhimmiyar hanyar fitar da man saudiyya bayan da Iran ta hana zirga-zirgar jiragen dakon mai a mashigar Hormuz, cewar Gulf News.

Kara karanta wannan

Trump ya juyo kan Najeriya, Amurka ta sake turo daruruwan sojoji, jiragen yaƙi ƙasar

Saudiyya ta sallami jami'an diflomasiyyar Iran a kasar
Dan Sarkin Saudiyya, Muhammad Bn Salman da Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran. Hoto: Inside the Haramain, Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Alakar Saudiyya da Iran ta kai makurar lalacewa

Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan, ya bayyana cewa alakarsu da Iran ta “lalace,” yana mai jaddada cewa kasarsa na da ikon kare kanta daga duk wata barazana.

Ya kuma gargadi cewa ci gaba da hare-haren Iran zai kara tsananta rikici tare da jawo mummunan sakamako ga dangantakar kasashen biyu a yanzu da nan gaba.

Wannan na zuwa ne bayan Qatar ma ta dauki irin wannan mataki, inda ta kori wasu jami’an tsaron ofishin jakadancin Iran a Doha sakamakon rikicin da ke kara kamari a yankin.

Kasashen Larabawa sun soki harin Iran a Syria

A wani labarin, kasashen Larabawa ciki har da Saudiyya sun yi Allah wadai da harin Isra’ila kan Syria a yankin Gabas ta Tsakiya.

Larabawan sun yi kira ga duniya ta dauki matakin gaggawa kan Isra'ila saboda saba dokokin kasa da kasa da ta ke yi.

Isra’ila ta ce harin ya biyo bayan kai hare-hare kan kabilar Druze a Sweida, yayin da Syria ta zargi kasar da karya dokokin kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.