Ana tsakiyar Yaki da Iran, An Fara Fuskantar 'Azabar' da ba a Taba Gani ba a Amurka

Ana tsakiyar Yaki da Iran, An Fara Fuskantar 'Azabar' da ba a Taba Gani ba a Amurka

  • An fara azababben zafin rana, wanda ba a taba kamarsa ba a tarihi a yammacin Amurka, lamarin da aka danganta shi da sauyin yanayi
  • Rahotanni sun nuna cewa yanayin zafin ya karya tarihi a jihohi da dama ciki har da California da Arizona, duk a kasar Amurka
  • Masana sun ce irin wannan zafi mai tsanani, wanda ya zo a daidai lokacin da Amurka ke yaki da Iran, yana faruwa ne sau daya cikin shekaru 500

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Washington – Wani zafin rana mai tsanani ya fara azabtar da mutane a Yammacin Amurka yayin da kasar ke tsakiyar yaki da Iran.

Yanayin zafin ya karya tarihin yadda aka saba, inda masana suka ce irin wannan lamari na faruwa ne sau daya cikin shekaru 500, kuma yana da nasaba da sauyin yanayi da mutane ke jawo wa.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuya: Dole ta sanya Trump yi wa Iran abin alheri

Zafin rana.
Yadda rana ke zafi da haske a sararin samaniya Hoto: Mateusz Slodkowski
Source: Getty Images

Channels tv ta tattaro cewa zafin ya ci gaba da karuwa a wannan mako, kuma ana sa ran zai wuce duk yadda ake tsammani zuwa karshen makon nan, yana kuma bazuwa zuwa wasu yankuna na gabashin Amurka.

A ranar Juma’a, wurare hudu a yankin hamada kusa da iyakar jihohin California da Arizona, zafin ya kai digiri 44.4 na Celsius, wanda ba a taba ganin irinsa ba a watan Maris a Amurka.

Yadda aka fara tsananin zafi a Amurka

A kalla birane 65 na fama da zafin da ba a taba ganin kamarsa ba a watan Maris, daga jihohin Arizona da California har zuwa Idaho.

Zafin da aka shiga a garin Death Valley ya kai 40°C a ranar Alhamis, yayin da birnin San Francisco, wanda aka fi sani da sanyi da hazo, ya kai 29°C.

A Colorado ma, masu wasan dusar kankara sun rika hawa tsaunuka ba tare da riga ba saboda tsananin zafi.

Kara karanta wannan

"Ba za a ga watan Shawwal da idanu ba": Masani ya yi magana ana shirin Sallah

Hukumar kula da yanayi ta Amurka ta fitar da gargadi kan tsananin zafi a yankin kudu maso yamma, daga Los Angeles zuwa Las Vegas.

An kuma gargadi jama’a da kada su bar yara ko dabbobi a cikin motoci saboda hatsarin da zafin ke haifarwa, cewar rahoton RFI.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Masana sun fadi dalilin zafin Amurka

Masana kimiyyar yanayi sun bayyana cewa wannan zafi ba zai yiwu ba a wannan lokaci na shekara ba tare da tasirin sauyin yanayi da dan Adam ke haddasawa ba.

Kungiyar World Weather Attribution ta ce irin wannan zafi mai tsanani ana tsammanin faruwarsa sau daya ne cikin shekaru 500.

Daya daga cikin masu binciken, Farfesa Friederike Otto, ta ce:

“Sauyin yanayi na tura yanayi zuwa matakai masu tsauri da ba a taba tsammani ba kuma ba a taba ganin irinsa ba a baya.”

Trump ya yi maganar tsagaita wuta

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan batun tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da Iran.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock

Shugaba Trump ya kuma bayyana cewa Isra'ila za ta amince ta kawo karshen yakin gaba daya idan Amurka ta yanke shawarar hakan.

Kalaman Donald Trump na zuwa ne yayin da jami'an Amurka suka ce kari dakarun sojan ruwa na suna kan hanyarsu ta zuwa Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262