Iran Ta Farmaki Jirgin Saman Yakin Isra'aila a Sararin Samaniya, an Ji Abin da Ya Faru
- Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi ikirarin yi wa Isra'ila barna a sararin samaniya
- IRGC ta yi ikirarin cewa dakarunta sun harbi wani jirgin saman yaki na Isra'ila samfurin F-16 a sararin samaniyar Iran
- Rundunar sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa jirgin saman yakin ya fuskanci barazana lokacin da yake shawagi a sararin samaniyar Iran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi iƙirarin cewa dakarunta sun harbi wani jirgin saman yaƙin Isra'ila samfurin F-16.
Rundunar IRGC ta bayyana cewa dakarunta sun harbi jirgin saman yakin ne lokacin da ya ke shawagi a sararin samaniyar Iran a safiyar yau, Asabar, 21 ga watan Maris 2026.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta kasar Iran fa kawo rahoton ikirarin rundunar IRGC na harbin jirgin a ranar Asabar, 21 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan
Ana cikin murnar Sallah, Iran ta shammaci Amurka da Isra'ila a sababbin hare hare
IRGC ta yi ikirarin harbin jirgin Isra'ila
Harbin jirgin saman yakin shi ne karo na uku da irin wannan lamari ya faru a lokacin wannan yakin, tashar Aljazeera ta dauko labarin.
A cewar IRGC, dakarun sun harbi sama da abubuwa 200 masu shawagi a sararin samaniyar Iran a lokacin yaƙin, ciki har da jirage marasa matuƙa, makamai masu linzami na, jiragen loda mai, da kuma jiragen yaƙi.
Me Isra'ila ta ce kan lamarin?
Tun da farko, rundunar sojojin Isra'ila a shafinta na X ta amince da cewa ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ya fuskanci harbi daga ƙasa a sararin samaniyar Iran.
Amma ta ce jirgin ya gano barazanar, ba a samu wata barna ba, kuma ya kammala aikinsa kamar yadda aka tsara.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"A lokacin gudanar da samamen rundunar sojin sama a sararin samaniyar Iran, an gano harbin makamin linzami daga ƙasa zuwa sama da aka nufi wani jirgin yaƙin Isra'ila."

Kara karanta wannan
Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila
"Ma'aikatan jirgin sun yi aiki daidai da ƙa'idojin tsaro, ba a samu wata barna ga jirgin ba, kuma an kammala aikin kamar yadda aka tsara."
"Tun farkon fara yaƙin, an yi yunƙuri da dama na harbin jiragen yaƙin Isra'ila a sararin samaniyar Iran, kuma dakarun sojojin saman sun yi nasarar tunkarar waɗannan barazanar."
"Rundunar sojojin sama za ta ci gaba da shawagi tare da kai hare-hare duk inda ake buƙata a faɗin Iran, kuma za ta kammala ayyukanta duk da barazanar da ke tattare da kowane samamen yaƙi."

Source: Getty Images
Iran ta harba makamai kan Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta sanar da gudanar da rukuni na 70 na harin ramuwar gayya da ta sanyawa suna 'Operation True Promise 4'.
Rundunar IRGC ta ce sabon farmakin ya nufi wurare sama da 55 da Amurka da gwamnatin Isra'ila suka mamaye a faɗin yankin.
Rundunar ta ce an kai hare-haren ne ta hanyar amfani da tsarin makamai masu linzami na Qiam da Emad tare da jirage marasa matuka.
Asali: Legit.ng