Iran Ta Bude Hanya, Sojojin Denmark za Su Gwabza Fada da Dakarun Amurka
- Dakarun kasar Demmark sun bayyana shirye-shiryen da suka fara domin hana shugaban Amurka, Donald Trump mallakar tsibirin Greenlad
- Bayan dawowar Donald Trump mulki karo na biyu, ya sha alwashin mallakar yankin, inda ya ce yana da muhimmanci ga tsaron Amurka
- Kasar Demnark da kasashen Turai sun nuna damuwa game da barazanar Trump, musamman bayan shiga kasar Venezuela da karfi da ya yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Greenland - Rahoto ya nuna cewa sojojin Denmark sun shirya tarwatsa filayen jiragen sama na Greenland domin hana Amurka kwace yankin.
Hakan na zuwa ne bayan tsananta barazana da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi game da karbar yankin saboda cewa yana da muhimmanci a gare su.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa hankalin Denmark ya tashi sosai ne bayan ganin Trump ya nuna karfin soja wajen shiga Venezuela da kama shugabanta.
Shirin Denmark na yaki da Amurka
Sojojin Denmark sun tsara wani shiri na amfani da abubuwan fashewa domin lalata titunan saukar jiragen sama a Greenland, domin hana yiwuwar mamayar Amurka, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito.
Rahoton ya bayyana cewa Denmark ta tura sojoji zuwa Greenland tare da abubuwan fashewa da kayan jinya domin shirye-shiryen aiwatar da wannan shiri idan Amurka ta yi yunkurin mamaye ta.
An ce wannan shiri ya samo asali ne yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke kokarin mallakar yankin mai fadin kusan kilomita miliyan 2.2, wanda ke karkashin ikon Denmark sama da shekaru 300.

Source: Getty Images
Bugu da kari, an kai kayan jinya domin kula da wadanda za su jikkata idan fada ya barke, alamar cewa an dauki shirin da matukar muhimmanci.
Ma’aikatar tsaron Denmark ba ta bayar da wani bayani kan batun ba, yayin da wani babban jami’in soja ya ce mutane kalilan ne suka san da wannan shiri saboda dalilan tsaro.
Amurka da Denmark suna cikin NATO
Amurka da Denmark dukkansu mambobi ne na kungiyar tsaron NATO, amma batun Greenland – wanda ke da ikon kai tsaye amma karkashin Denmark – ya jawo sabani tsakanin Amurka da kawayenta na Turai.
Trump ya sha bayyana sha’awarsa na hade Greenland da Amurka, amma shugabannin Turai da Denmark sun yi watsi da bukatar.
Rahoto ya kuma ce Denmark ta nemi goyon bayan kasashen Turai kamar Faransa da Jamus domin nuna hadin kai, tare da kara ayyukan soja a yankin.
An kara tsananta damuwa ne bayan wani lamari a ranar 3 ga Janairun 2026, bayan kalaman Trump na cewa yana son mallakar Greenland saboda muhimmancin tsaro.
Amurka ta cirewa Iran takunkumi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta cire takunkumin man fetur da ta sanyawa Iran a shekarun baya.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Trump ta janye takunkumin ne biyo bayan tashin farashin mai a Amurka bayan Iran ta toshe mashigar Hormuz.
A yanzu haka dai kasashe da dama za su samu damar sayen man fetur daga Iran a tsawon kwana 30 da Amurka ta dauke takunkumin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

