An Zo Wajen: Trump Ya Yi Magana kan Tsagaita Wuta a Yakin Amurka, Isra'ila da Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan batun tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da Iran tare da hadin gwiwar Isra'ila
- Donald Trump ya kuma tabo batun yiwuwar Amurka ta kwace tsibirin Kharg na Iran domin matsa mata lamba ta bude mashigar ruwa ta Hormuz
- Shugaba Trump ya kuma bayyana cewa Isra'ila za ta amince ta kawo karshen yakin idan Amurka ta yanke shawarar hakan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da Iran.
Shugaba Donald Trump ya yi watsi da batun tsagaita wuta da Iran, a yakin da ake gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce Shugaba Donald Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan
China ta gaza hakuri, ta sake yunkurowa kan yakin Amurka da kasar Musulunci ta Iran
Trump na duba yiwuwar kwace tsibirin Kharg
Kalaman Trump na zuwa ne yayin da jami'an Amurka suka ce karin dakarun sojan ruwa na "Marines" suna kan hanyarsu ta zuwa Gabas ta Tsakiya, wanda hakan na zama alamar yiwuwar ƙaddamar da samame ta ƙasa bayan makonni uku da fara yaƙin.
Wuri ɗaya da dakarun ka iya nufa shi ne tsibirin Kharg na Iran, inda fadar White House ta bayyana cewa Amurka na iya "ƙwace" wannan babbar cibiyar man fetur a kowane lokaci idan Trump ya ga dama.
Tashar Axios ta ruwaito cewa Trump yana duba yiwuwar mamaye ko killace tsibirin domin matsa wa Tehran lamba ta sake buɗe muhimmiyar mashigar Hormuz.
Me Trump ya ce kan tsagaita wuta da Iran?
Trump ya bayyana cewa, “Ina iya kasancewa da shiri ko kuma akasin haka,” amma ya ƙi bayyana wa manema labarai takamaiman matsayinsa.
Shugaba Trump ya kuma bayyana Kharg a matsayin “tabbas wuri ne da mutane ke magana a kai. Amma ba zan iya gaya muku komai ba.”
“Za mu iya yin tattaunawa, amma ba na son tsagaita wuta. Ba a tsagaita wuta lokacin da kake kusan shafe ɗayan ɓangaren baki ɗaya."
- Shugaba Donald Trump

Source: Getty Images
Shin Isra'ila za ta yarda a kawo karshen yakin?
Jaridar The Times of Israel ta ce lokacin da aka tambaye shi ko Isra'ila za ta amince ta kawo ƙarshen yaƙin idan Amurka ta yanke shawarar yin hakan, Trump ya amsa da cewa:
“Ina jin haka, kwarai kuwa. Dangantakar tana da kyau sosai. Muna son abubuwa kusan iri ɗaya. Kun san me muke so? Muna son nasara mu duka biyun kuma abin da muka samu ke nan."
Iran ta gano makircin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran addinin Musulunci a Jamhuriyar Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya haska wani makirci da ake shiryawa yayin da ake ci gaba da yaki da Amurka, Isra'ila.
Mojtaba Khamenei ya bayyana damuwa kan makircin da ake kullawa Iran a yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jagoran addinin ya bayyana cewa hare-haren da aka kai Turkiyya da Oman da cewa ba su da alaka da sojojin Iran.
Asali: Legit.ng
