Iran Ta Yi Babban Rashi a Ranar Sallah, Kakakin Rundunar IRGC Ya Mutu a Harin Isra'ila

Iran Ta Yi Babban Rashi a Ranar Sallah, Kakakin Rundunar IRGC Ya Mutu a Harin Isra'ila

  • Hi An kashe kakakin rundunar IRGC Ali Mohammad Naeini a Tehran yau Juma'a, bayan ya yi barazanar cewa Iran za ta ci gaba da kera makamai
  • Kisan Naeini ya biyo bayan mutuwar manyan jami'an tsaron Iran guda uku a wannan makon yayin da Amurka da Isra'ila ke rura wutar yaki
  • Hare-hare kan matatun iskar gas a yankin Gulf na barazanar dakatar da kashi 20 cikin 100 na makamashin duniya yayin da yaki ke tsananta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Rundunar IRGC ta tabbatar da mutuwar kakakin rundunar, Brigadier Janar Ali Mohammad Naeini, sakamakon harin hadin gwiwar Amurka da Isra'ila.

IRGC ta siffanta harin a matsayin "aikin ta'addanci da matsorata suka aikata," a birnin Tehran jim kaɗan bayan da Naeini ya fitar da wani gargaɗi ga Shugaba Donald Trump.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta kira ruwa, Iran ta kaddamar da sababbin hare hare masu zafi

Isra'ila ta kashe kakakin rundunar sojojin Iran a wani .hari da ta kai birnin Tehran
Kakakin rundunar tsaron Iran ta IRGC, Janar Ali Mohammad Naeini, yana jawabi a Tehran. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Image
Source: Getty Images

Isra'ila/Amurka sun kashe kakakin IRGC

Kafar watsa labarai ta Aljazeera ta rahoto cewa, Birgediya Janar Naeini ya bakunci lahira ne a harin hadin gwiwar Amurka da Isra'ila da asubahin yau Juma'a.

Jim kadan kafin mutuwarsa, Naeini ya gargadi Trump game da lalata ƙarfin sojin ruwan Iran, sannan ya jaddada cewa kera makaman linzamin ƙasar bai tsaya ba duk da rikicin da ake ciki.

Yayin da Isra'ila ba ta yi bayani a hukumance kan wannan farmakin ba, rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta tabbatar da kakkabe wasu manyan jami'an Iran kwanan nan a matsayin ɓangare na tsananta yaƙin kawar da shugabannin gwamnatin ƙasar biyo bayan mutuwar babban jagora Ayatollah Ali Khamenei a ranar 28 ga Fabrairu.

Janar Naeini, wanda ya kasance mai magana da yawun rundunar IRGC tun shekarar 2024, babban jigo ne a fannin dabarun "yaƙi" na Iran da ayyukan yaƙin da ba na makami ba.

Kara karanta wannan

Iran ta samu nasara, sababbin makamanta sun yi gagarumar barna a Isra'ila

Gargadin da Naemi ya yi wa Trump

Sa'o'i kaɗan kafin mutuwarsa, ya ƙalubalanci Amurka da ta tura jiragen ruwa zuwa tekun Fars "idan sun isa," yana mai watsi da ra'ayoyin ƙasashen Yamma na cewa ƙarfin sojin Iran ya ragu.

"Masana'antar makamanmu ta cancanci cikakken maki... ko a lokacin yaƙi, muna ci gaba da kera su," in ji Naeini kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito.

Kisan sa shi ne babban rauni na huɗu da tsarin shugabancin Tehran ya samu a wannan makon, bayan mutuwar Ministan Leken Asiri Esmaeil Khatib, jigon tsaro Ali Larijani, da shugaban Basij Gholamreza Soleimani.

Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya riga ya yi alkawarin "abubuwan mamaki" ga shugabannin Iran, yana mai cewa ayyukan nasu na nufin ruguza "tsarin ta'addancin" gwamnatin ƙasar, in ji rahoton The Logical Indian.

IRGC ta ce kisan Brigadier General Ali Mohammad Naeini aikin matsorata ne.
Kakakin rundunar tsaron Iran ta IRGC, Brigadier General Ali Mohammad Naeini, yana jawabi a Tehran. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Image
Source: Getty Images

Yadda yakin Iran da Amurka ya tsananta

Kawar da Naeini na daga cikin babban yaƙin da ke ta'azzara cikin sauri wanda ya fara da gagaruman hare-haren Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

A wannan lokaci, an ga gagarumin sauyi a siyasance a Gabas Ta Tsakiya, inda Iran ke mayar da martani ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da makaman linzami kan Isra'ila da ƙasashen Larabawa dake karɓar bakuncin dakarun Amurka.

Rikicin ya ɗauki sabon salo na tattalin arziki kwanan nan, tare da hare-hare kan matatar iskar gas ta Ras Laffan a Qatar da filin iskar gas na South Pars a Iran, wanda ke barazanar dakatar da kusan 20% na makamashin duniya dake ratsa mashigin Hormuz.

Isra'ila ta kashe wani kwamandojin Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, Isra'ila ta kashe Birgediya Janar Abdullah Jalali Nasab da Amir Shariat a wani harin sama da ta kai kan cibiyar leken asiri a birnin Tehran.

Wadannan kwamandoji ne ke da alhakin nazarin bayanan sirri na yaki da Isra'ila kuma kisan su babban koma-baya ne ga tsaron Iran.

Kasar Iran dai ta rasa manyan kwamandojin tsaro da suka hada da Ministan Tsaro da Shugaban IRGC tun bayan barkewar wannan babban yaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com