Ta Fasu: Shirin da Trump Yake Yi don Matsawa Iran Lamba Ta Saduda kan Hormuz
- Iran na ci gaba da nuna iko a mashigar ruwa ta Hormuz wadda ke da muhimmanci wajen jigilar man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya
- Kulle mashigar da Iran ta yi ya jawo an samu tashin farashin danyen mai da sauran kayan makamashi a duniya
- Wasu majiyoyi daga gwamnatin Amurka, sun bayyana cewa Shugaba Donald Trump, na shirin matsawa Iran lamba ta bude mashigar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Gwamnatin Donald Trump tana duba wasu tsare-tsare na mamaye ko killace tsibirin Kharg na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Gwamnatin Trump tana duba yiwuwar hakan ne domin matsa wa ƙasar Iran lamba ta buɗe Mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Tashar Axios ta bayyana cewa wasu majiyoyi huɗu masu masaniya kan lamarin suka shaida mata hakan.
Wane shirin Trump ke yi kan Iran?

Kara karanta wannan
Hukumar leken asirin Amurka ta gano gaskiya, ta 'kunyata' Trump kan shirin nukiliyar Iran
Shugaba Trump ba zai iya kawo ƙarshen yaƙin ba, aƙalla bisa sharuɗɗansa, har sai ya ga ya karya ikon da Iran ke da shi na toshe hanyoyin jigilar kayayyaki ta mashigar.
A halin yanzu kuma, farashin makamashi a duniya yana ta tashi sama sosai.
Sai dai, duk wani farmaki na kwace tsibirin Kharg, wanda ke da nisan mil 15 daga gaɓar teku kuma yake tace kashi 90 na danyen mai ɗin da Iran ke fitarwa, na iya jefa dakarun Amurka kai-tsaye cikin hatsarin yaƙi.
Don haka, irin wannan farmakin zai kasance ne kawai bayan rundunar sojojin Amurka ta ƙara raunana ƙarfin sojin Iran a kewayen Mashigar Hormuz.
Me Amurka ta ke bukata?
"Muna buƙatar kusan wata guda don ƙara raunana Iran da hare-hare, mu ƙwace tsibirin, sannan mu matsa musi lamba domin mu yi amfani da hakan wajen tattaunawa."
Irin wannan farmakin, idan aka amince da shi, zai buƙaci ƙarin dakarun sojoji. Tuni rukunonin sojojin ruwa guda uku mabanbanta suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.
A cewar wani jami'in Amurka, Fadar White House da Ma'aikatar tsaro ta Pentagon suna duba yiwuwar tura karin dakarun nan ba da jimawa ba.
Wani babban jami'i a gwamnatin Trump ya bayyana cewa:
"Yana son a buɗe Hormuz. Idan har dole sai ya ƙwace tsibirin Kharg don hakan ta faru, to hakan za ta kasance. Idan ya yanke shawarar yin mamaya ta gaɓar teku, hakan ma za ta faru."
"Amma har yanzu ba a riga an yanke wannan shawarar ba. A koyaushe muna tura dakarunmu na ƙasa a lokacin rikice-rikice a ƙarƙashin kowane shugaban ƙasa, har da Trump."
"Na san wannan abin damuwa ne ga kafofin yaɗa labarai, kuma na fahimci siyasar da ke tattare da hakan, amma shugaban ƙasa zai yi abin da yake daidai."

Source: Facebook
An gano hikimar Trump
Sanata Tom Cotton wanda ke shugabantar kwamitin leken asiri na majalisar dattawa, ya ce Trump ya yi "hikima" da bai cire batun mamaya ta ƙasa daga lissafi ba, kodayake bai bayyana ko yana goyon bayan hakan ba.
Tom Cotton ya jaddada cewa rufe mashigar wani mataki na gaggawa da Iran ta ɗauka, amma ya ce Trump yana da tarin tsare-tsare don tunkarar matsalar, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.
Yayin da tsibirin Kharg yake da matuƙar muhimmanci ga masana'antar man fetur ta Iran, babu tabbas cewa ƙwace shi zai gamsar da Tehran ta amince da zaman lafiya bisa sharuɗɗan Trump.
Iran ta kai hare-hare kan Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta ƙaddamar da rukuni na 65 na harin ramuwar gayya da take kira Operation True Promise 4.
Rundunar IRGC ta kai hari kan matatun man fetur na Isra'ila tare da gabatar da sabon makamin linzami mai cin dogon zango da ake kira “Nasrallah” wanda ke ɗauke da bama-bamai masu yawa.
Makamin na Nasrallah nau'i ne na zamani wanda aka inganta daga makamai mai linzami na Qadr da Iran ke amfani da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

