Isra'ila Ta Kira Ruwa, Iran Ta Kaddamar da Sababbin Hare Hare Masu Zafi
- Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), ta kaddamar da sababbin hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka
- IRGC ta bayyana cewa ta farmaki wasu wurare a Isra'ila tare da sansanonin sojojin Amurka da ke a yankin Gabas ta Tsakiya
- Rundunar IRGC ta kuma aika da gargadin cewa ba ta za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da kaddamar da rukuni na 66 na harin ramuwar gayya da take ci gaba da kai wa mai suna 'Operation True Promise 4'.
Hare-haren sun haɗa da harba manyan makamai masu linzami da dama da suka nufi wurare daban-daban a yankunan Isra'ila da kuma sansanonin sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin hulda da jama'a na rundunar IRGC ya fitar ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.
Iran ta ce hare-harenta kan Isra'ila sun yi nasara
Ofishin ya bayyana cewa an gudanar da wannan sabon hari cikin "nasara," inda aka farmaki wuraren da ke tsakiya da kuma Kudancin Isra'ila, ciki har da birnin Tel Aviv, da kuma sansanonin sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar ta ba da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da haɗakar tsarin makamai masu linzami, ciki har da babban makami mai linzami na Qadr da ke ɗauke da bama-bamai da dama.
Makaman da Iran ta harba
Hakazalika an yi amfani makamai masu linzami na Khorramshahr da Kheibar Shekan, da kuma makaman Qiam masu cin matsakaicin zango.
A cewar sanarwar, rukuni na 66 ya kuma haɗa da harba makamai masu linzami na Zolfaqar da kuma jirage marasa matuƙa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, hukumomin Isra'ila, a ƙoƙarin su na shawo kan gazawar da suka yi a baya da kuma rikice-rikicen cikin gida, gami da badakalar Epstein, sun shiga wani "yaƙi na zalunci da Iran" wanda tun farko aka ƙaddara masa faɗuwa.
Iran ta yi gargadi ga Amurka, Isra'ila
Sanarwar ta kammala da wani gargaɗi:
“Ba za mu bar ku ba; wannan ramuwar gayya za ta ci gaba."

Source: Twitter
Harin Operation True Promise 4 ya fara ne jim kaɗan bayan hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Wannan ramuwar gayya ta shafi wurare masu muhimmanci da na dabarun yaƙi a tsakiyar Isra'ila ciki har da birnin Tel Aviv, birni mai tsarki na al-Quds, tashar jirgin ruwa ta Haifa, Be'er Sheva da yankin hamada na Negev.
Iran ta fadi shirinta kan Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi magana kan shirin da ta yi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Babban kwamanda a rundunar sojojin Iran, Manjo Janar Ali Abdollahi, ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da abubuwan mamaki da ta tanada ga Shugaban Amurka Donald Trump.
Manjo Janar Ali Abdollahi ya bayyana cewa suna da abubuwan ban mamaki da suka shirya kan Trump da kasar Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

