Isra'ila Ta Shiga Uku, Iran Ta Kaddamar da Sabon Makami Mai Hatsari
- Rundunar IRGC ta kasar Iran ta ci gaba da kai harin ramuwar gayya wanda ta sanyawa sunan 'Operation True Promise 4' kan Isra'ila da Amurka
- A karo na 65 na hare-haren da IRGC ke kai wa, ta kaddamar da sabon makami mai linzami wanda yake cin dogon zango
- Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta farmaki wasu matatun mai na Isra'ila da kuma sansanonin sojojin Amurka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ƙaddamar da rukuni na 65 na harin ramuwar gayya da take kira Operation True Promise 4.
Rundunar IRGC ta kai hari kan matatun man fetur na Isra'ila tare da gabatar da sabon makamin linzami mai cin dogon zango da ake kira “Nasrallah” wanda ke ɗauke da bama-bamai masu yawa.

Source: Twitter
Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar ranar Alhamis, 19 ga watan Maris 2026.
Wuraren da Iran ta farmaka a Isra'ila
IRGC ta ce sabon harin ya nufi matatun man fetur na Ashdod da Haifa, waɗanda ke cikin manyan matatun gwamnatin Isra'ila, inda aka yi amfani da makamai mai linzami na Nasrallah a karon farko.
Makamin na Nasrallah nau'i ne na zamani wanda aka inganta daga makaman linzami na Qadr da aka yi amfani da su a hare-haren baya kan sansanonin sojojin Amurka a yankin da kuma yankunan da Isra'ila ta mamaye.
Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan hari karo na 65 ya yi amfani da nau'o'in makamai masu linzami masu cin dogon zango da aka ƙera a cikin gida a Iran.
Ya zuwa yanzu, IRGC ta yi amfani da makamai masu ƙarfin gaske a hare-haren baya-bayan nan, da suka haɗa da makamai masu linzami na Qadr, Kheibar Shekan, Emad, da kuma Haj Qassem.
Wadanne makamai aka yi amfani da su?
A cewar sanarwar, sabon harin ramuwar gayyar ya kuma yi amfani da makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango na Qiyam da Zolfaghar wajen farmakar sansanin sojojin saman Amurka na Al Kharj da ke Saudi Arabia.
Sansanin sojojin shi ne babbar cibiyar kai-da-kawowa da loda wa jiragen yaƙi na F-16 da F-35 mai, gami da jiragen leƙen asiri na AWACS.

Source: Getty Images
Bugu da ƙari, irin waɗannan makaman linzamin sun nufi sansanin Fujairah Sheikh Isa da ke Hadaddiyar daular Larabawa (UAE), wanda ke zaman babban ofishin gudanarwa da sarrafa bayanai da kuma cibiyar sadarwa ta sojojin Amurka a yankin.
Dakarun sojojin Amurka da ke sansanin al-Zafra a UAE, waɗanda suka taka rawar goyon baya da leƙen asiri a harin da aka kai wa Iran, su ma sun fuskanci hare-haren makami mai linzami na Qiyam, Zolfaghar, da kuma Kheibar Shekan mai cin dogon zango.
Makaman Iran sun sauka a Isra'ila
Tashar Aljazeera ta ce Isra'ila ta tabbatar da cewa harin makaman Iran ya sauka a matatar mai da ke Haifa.
Ministan makamashi, Eli Cohen ya bayyana cewa an samu daukewar wuta na wani dan lokaci amma daga baya an dawo da ita.
Iran ta yi ikirarin lalata jirgin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta Iran ta yi ikirarin kai hari kan jirgin saman yaki na Amurka.
Rundunar IRGC ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan jirgin saman yaki na Amurka samfurin F-35 tare da lalata shi.
Rundunar sojojin Amurka ta tabbatar da cewa jirgin ya samu matsala a sararin samaniyar Iran amma ya yi saukar gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


