Wuta Ta Yi Wuta: Iran Ta Yi Ikirarin Lalata Babban Jirgin Yakin Amurka
- Rundunar kare dakarun juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi ikirarin yi wa Amurka barna a yakin da ake yi
- IRGC ta yi ikirarin cewa ta kai farmaki kan jirgin saman yaki na Amurka lokacin da yake shawagi a sararin samaniyar Iran
- Mahukunta a Amurka sun tabbatar da cewa jirgin ya samu matsala lokacin da yake gudanar da aiki a kasar Iran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai hari kan wani jirgin saman yaki na Amurka.
Rundunar IRGC ta yi ikirarin kai hari tare da “lalata” wani jirgin saman yaƙin Amurka samfurin F-35.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton ikirarin na rundunar IRGC a ranar Alhamis, 19 ga watan Maris 2026.
Wasu majiyoyi biyu sun shaidawa tashar CNN cewa wani jirgin saman yaƙi na Amurka samfurin F-35 ya yi saukar gaggawa a wani sansanin jiragen sama na Amurka da ke Gabas ta Tsakiya bayan da aka harbe shi da abin da ake ganin makamin Iran ne.
Me Amurka ta ce kan lamarin?
Kyaftin Tim Hawkins, kakakin rundunar Centcom ta Amurka, ya ce jirgin yaƙin na zamani mai dabarun ɓoye wa na'urar bin diddigi yana gudanar da aikin yaƙi ne a sararin samaniyar Iran lokacin da aka tilasta masa saukar gaggawa.
Hawkins ya ce jirgin ya sauka lami-lafiya kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.
“Jirgin ya sauka lami-lafiya, kuma matuƙin jirgin yana cikin yanayi mai kyau. Ana gudanar da bincike kan wannan lamari.”
- Kyaftin Tim Hawkins
Wannan lamari zai kasance karo na farko da Iran ta taba jirgin Amurka a yaƙin da aka fara tun ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Amurka da Isra'ila duka suna amfani da jiragen F-35 a cikin wannan rikici; farashin jirgi ɗaya ya haura dala miliyan 100.
Amurka ta rasa jirage a yaki da Iran
Amurka ta rasa wasu jiragen a yaƙin ya zuwa yanzu, kodayake babu wanda aka sani cewa makiya ne suka harbe shi.
Jiragen yaƙi na Amurka F-15 guda uku ne dakarun kariya na Kuwait suka harbe su bisa kuskure, inda dukkan ma'aikata shida suka fito lami-lafiya.

Source: Getty Images
Sannan a makon da ya gabata, wani jirgin loda mai na KC-135 Stratotanker ya faɗi a yammacin Iraƙi, kodayake har yanzu ba a bayyana dalilin ba.
Rundunar sojin Amurka ta ce lamarin ba ya da alaƙa da harbin makiya ko na abokan tafiya. Dukkan ma'aikata shida da ke cikin jirgin na KC-135 sun rasa rayukansu.
Yayin da yaƙin ke gab da kammala mako na uku, manyan jami'an Amurka suna ci gaba da iƙirarin samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da Iran.
Ministan tsaro, Pete Hegseth, ya bayyana a safiyar Alhamis cewa Amurka tana “samun nasara sosai” sannan kuma an ruguza tsarin kariya na sararin samaniyar Iran.
Gwamnatin Amurka na neman kudin yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatar tsaron Amurka, wato Pentagon, ta bukaci Fadar White House da ta amince da wani sabon kasafin kudi don ci gaba da yaki da Iran.

Kara karanta wannan
Ana rade radin ya mutu, Jagoran addinin Iran ya yi nadin da zai iya rikita Amurka da Isra'ila
Ma'aikatar Pentagon na neman kudin da ya haura Dala biliyan 200 domin ci gaba da daukar nauyin yakin Iran.
Wata majiya mai karfi a gwamnatin ta bayyana cewa wannan kudin ya haura abin da aka kashe a hare-haren sama da aka yi a baya-bayan nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

