"Kasashe za Su Samu Matsala": Iran Ta Rubuta Wasika ga Majalisar Dinkin Duniya

"Kasashe za Su Samu Matsala": Iran Ta Rubuta Wasika ga Majalisar Dinkin Duniya

  • Kasar Iran ta bayyana takaici game da halin ko-in-kula da Majalisar Dinkin Duniya ke nuna wa game da hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata
  • Abin da ya fi ba ta takaici shi ne yadda ta yi zargin cewa Majalisar Dinkin Duniya da yin shiru kan kashe manyan jami’anta
  • Kasar ta ce shirun da aka yi na ƙarfafa Isra’ila wajen kai irin wadannan hare-hare, kuma kashe-kashen na iya zama ruwan dare a duniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kasar Iran – Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir-Saeid Iravani, ya aike da wata takarda ga Kwamitin Tsaro na Majalisar.

A cikin takardar, ya yi zargin cewa Majalisar ta ja bakinta ta rufe yayin da Amurka da Isrra'ila ke kashe manyan jami’an ƙasarsa.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Iran ta fusata da shirin Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Kasar Musulunci ta Iran, Masoud Pazeshkian Hoto: Masoud Pazeshkian
Source: Facebook

Aljazeera ta wallafa cewa Iravani ya nuna damuwa matuka kan yadda Majalisar ke nuna halin ko-in-kula game da hare-haren da ake kai wa kan jami’an Iran.

Zargin Iran kan shirin Majalisar Dinkin Duniya

India Today ta ruwaito jakadan ya ce rashin daukar mataki daga bangaren Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na kara bai wa Isra’ila karfin gwiwa wajen kai hare-hare kan manyan jami’an Iran. Ya bayyana cewa irin wannan shiru daga babbar cibiyar tsaro ta duniya na iya janyo matsala mai girma, domin yana nuna kamar an amince da irin wadannan hare-hare.

Iran ta ce shiru kan kashe manyanta zai zama matsala ga duniya
Jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei Hoto: Mojtaba Khamenei
Source: Getty Images

Iravani ya jaddada cewa ya kamata Majalisar ta tashi tsaye ta dauki mataki domin hana ci gaba da irin wannan ta'asa.

Ya nanata cewa wannan kisan na iya zama babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya ba Iran kadai ba.

Iran ta gargadi Majalisar Dinkin Duniya

Jakadan ya kuma yi gargadi cewa idan aka kyale irin wadannan kashe-kashe ba tare da hukunci ba, za su iya zama kamar al’ada a duniya.

Kara karanta wannan

Trump ya soki NATO, ya yi magana game da ƙasashen da suka ki taya su yaƙar Iran

A cewarsa, wannan na iya kai ga yadda kasashe za su rika kai hari kan jami’an juna ba tare da tsoron hukunci ba, lamarin da zai iya janyo rikici mai tsanani tsakanin kasashe.

Ya kara da cewa idan hakan ta faru, ba wai Iran kadai za ta fuskanci barazana ba, har ma da sauran kasashen duniya, musamman wadanda ke da sabani a tsakaninsu. Iran ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakan gaggawa domin dakile irin wadannan hare-hare, tare da tabbatar da cewa an kare dokokin kasa da kasa da ke hana kashe-kashen siyasa.

Trump ya magantu kan harin Isra'ila a Iran

A baya mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald J Trump ya yi gargadi kan rikicin Gabas ta Tsakiya bayan wani harin Isra'ila da filin gas da ke Iran.

Shugaban ya zargi Iran da kai hari kan Qatar ba tare da cikakken bayani a kan harin da aka mai wani wuri mai muhimmanci a kasarta ba inda ya ce an yui kuskure.

Ya ce Amurka za ta dauki mataki mai tsauri idan aka sake kai hari Qatar, tare da karin bayani game da mummunan harin Isra'ila da ya ce ba za a sake kai irinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng