Iran Ta Yi Luguden Wuta yayin da Larabawa ke tsaka da Taro a Saudiyya

Iran Ta Yi Luguden Wuta yayin da Larabawa ke tsaka da Taro a Saudiyya

  • A jiya Laraba, 18 ga watan Maris 2026 shugabannin kasashen Musulmi da Larabawa suka gudanar da taron gaggawa kan yakin Iran
  • Yayin da suke tsaka da taron, an ji saukar makaman Iran a birnin Riyadh, lamarin da ya jawo tashin hankali da martani daga mahalarta
  • Tun karshen watan Fabrairun 2026 Amurka da Isra'ila suka kaddamar a hari a kan Iran, lamarin da ke cigaba da shafar kasashen Gabas ta Tsakiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta yi martani kan hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki da take danganta su da Iran.

Rahotanni sun nuna cewa ministan harkokin wajen kasar, Faisal bin Farhan Al Saud, ya yi martani a ranar Alhamis inda ya yi gargadi cewa ci gaba da hare-hare na iya janyo martani kai tsaye.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta tsoma baki game da harin Iran kan kasashen Larabawa

Shugabannin Larabawa da kasashen Musulmi a taro
Yadda shugabannin Larabawa da kasashen Musulmi suka yi taro a Riyadh. Hoto: Anadolu Agency
Source: Facebook

A wani bidiyo da Al-Jazeera ta wallafa a shafinta na Facebook, Faisal bin Farhan Al Saud ya yi magana kan harin da Iran ta kai suna tsaka da taro a Riyadh.

Iran ta kai hari Larabawa na taro

Hukumomin Saudiyya sun bayar da rahoton wasu sabbin hare-hare a ranar Laraba, wanda ya zo daidai da lokacin taron diflomasiyya a babban birnin kasar.

‘Yan jarida sun ce an ji karar fashe-fashe da dama a fadin Riyadh, yayin da ma’aikatar tsaro ta ce ta samu nasarar kakkabo makamai masu linzami.

Yarima Faisal ya bayyana lokacin da aka kai hare-haren a matsayin sakon kai tsaye daga Tehran:

“Kai hari Riyadh yayin da wasu jakadu ke taro… shi ne mafi karfin shaida kan yadda Iran ke watsi da diflomasiyya,”

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa ya kara da cewa:

“Ba ta yarda da tattaunawa da makwabtan ta ba.”

Kara karanta wannan

Iran ta yi babbar barna da ta harba makamai kan jiragen Amurka a Saudiyya

Ministan harkokin wajen Saudiyya ya yi tir da abin da ya kira hare-hare akai-akai kan muhimman abubuwan more rayuwar fararen hula a yankin Gulf, ciki har da cibiyoyin makamashi, filayen jiragen sama, da gidajen zama.

Yadda aka yi wani taron kasashen Musulmi
Mahalarta wani taron kasashen Musulmi a 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kuma yi watsi da ikirarin Iran cewa tana kai hari ne kan kadarorin Amurka a yankin, yana mai cewa wannan hujja mai rauni ce, tare da jaddada cewa kasashen Gulf ba za su amince da haka ba.

Martanin Saudi kan harin Iran

Da yake magana bayan taron ministocin harkokin wajen yankin da aka gudanar a Riyadh, Yarima Faisal ya zargi Iran da kokarin matsa wa makwabtan ta lamba ta hanyar ci gaba da kai hare-hare.

“Saudiyya ba za ta mika wuya ga wannan matsin lamba ba, kuma a maimakon haka, kaikayi zai koma kan mashekiya,”

Inji shi.

Ya kara da cewa:

“Mun yi tanadin daukar matakin soja idan aka ga ya zama dole.”

Sultan ya caccaki Amurka/Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana game da hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kasar Iran.

Sultan ya bayyana cewa Iran tana da hakkin kare kanta a karkashin dokar majalisar dinkin duniya bayan harin da aka kai mata.

Ya zargi kasashen duniya da suka yi shiru bayan harin da Isra'ila da Amurka suka kai amma suka yi magana kan martanin Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng