Ali Larijani: Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei Ya Dauki Zafi, Ya Tura Sako ga Amurka da Isra'ila

Ali Larijani: Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei Ya Dauki Zafi, Ya Tura Sako ga Amurka da Isra'ila

  • Kisan shugaban Majalisar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ali Larijani, ya fusata jagoran addini na kasa, Mojtaba Khamenei
  • Jagoran na kasar Iran ya yi Allah wadai da kisan Ali Larijani da sauran manyan kwamandojin sojoji, wadanda ya kira da "shahidai"
  • Ya bayyana lamarin a matsayin aiki na “makiya masu aikata laifi” wadanda ya ce dole su dandana kudarsu bisa zubar da jinin shahidai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya fitar da sanarwa bayan kusan sa'o'i 24 da hukumomi suka tabbatar da kisan babban jami’in tsaro, Ali Larijani.

Gwamnatin Isra'ila ce ta fara ikirarin kashe Larijani a wasu hare-hare da ta kai a daren ranar Litinin da ta gabata, amma daga bisani hukumomin Iran suka tabbatar da hakan.

Jagoran addini.
Jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: anadolu
Source: Getty Images

Kisan Ali Larijani ya fusata Khamenei

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gargadin da Ali Larijani ya yi wa Amurka da Isra'ila kafin su kashe shi

Tashar Al-jazeera ta tattaro cewa a cikin sanarwar da ya fitar yau Laraba, Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa ya samu labarin mutuwar Larijani cikin “babban bakin ciki”

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai basira, jajirtacce kuma fitaccen jigo a siyasar kasar Musulunci ta Iran.

Jagoran Iran ya kara da cewa kisan irin wannan mutum na nuna muhimmancinsa da kuma irin kiyayyar da makiyan Musulunci ke yi masa.

A cewarsa, wannan hari ba zai raunana tsarin gwamnatin addinin Musulunci da Iran ke tafiya a kai ba, illa ma zai kara masa karfi.

Khamenei ya tura sako ga Isra'ila/Amurka

Mojtaba Khamenei ya yi gargadi mai tsauri ga wadanda ke da hannu a kisan, inda ya ce dole ne su fuskanci sakamakon abin da suka aikata.

A kalamansa, ya ce:

“Masu gaba da addinin Musulunci su sani cewa zubar da wannan jini da suke yi yana kara karfafa tsarin Jamhuriyar Musulunci ne, kuma kowanne jini yana da farashi da dole ne masu kisan shahidai su biya nan gaba kadan.”

Tasirin kisan Larijani ga siyasar Iran

Masu nazarin al’amuran siyasa sun bayyana cewa wannan kisan na Ali Larijani iya kara dagula yanayin tsaro a Iran tare da kara tsananta rikici tsakanin kasar da abokan gabanta.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da Soleimani, babban jami'in Iran da Isra'ila ta kashe

Haka kuma, kalaman jagoran na nuna yiwuwar daukar matakan ramuwar gayya ko tsaurara tsaro a cikin gida da waje, kamar yadda TRT World ta rahoto.

Ali Larijani.
Tsohon shugaban Majalisar tsaron kasar Iran, Marigayi Ali Larijani Hoto: AFP
Source: Getty Images

Har yanzu babu alamar za a fara zaman tattaunawa domin kawo karshen wannan yaki, wanda ya shiga rana ta 18 tun bayan fara kai hare-hare a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Isra'ila ta kashe minista a kasar Iran

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila ta yi ikirarin cewa hare-haren da ta kai sun hallaka Ministan leken asiri na kasar Iran, Esmaeil Khatib.

Isra'ila dai na zargin cewa Khatib ya taka muhimmiyar rawa lokacin zanga- zangar baya-bayan nan a duk faɗin Iran, ciki har da kamawa da kisan masu zanga-zanga.

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya tabbatar da cewa Isra'ila ta kashe Ministan leken asiri, Esmaeil Khatib, a wani hari da aka kai a daren jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262