Iran Ta Samu Nasara, Sababbin Makamanta Sun Yi Gagarumar Barna a Isra'ila
- Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Iran a yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran na harba makamai masu linzami zuwa biranen Isra'ila da wasu sansanonin sojojin Amurka da ke yankin
- Sababbin makamai masu linzami da Iran ta harba, sun samu nasarar sauka a birnin Tel-Aviv inda suka yi barna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Makamai masu linzami da Iran ta harba sun samu nasara ratsa kwararan matakan kariya na Isra'ila.
Makaman masu linzami na Iran sun yi barna mai yawa a Tel Aviv, inda suka kashe mazauna guda biyu tare da jikkata wasu kusan saba'in a daidai lokacin.

Source: Twitter
Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoton a ranar Laraba, 18 ga watan Maris 2026.
Makaman Iran sun sauka a Isra'ila
Rahotanni sun nuna cewa tun farkon sa'o'in ranar Laraba, makamai masu linzami na Iran sun faɗa wa birnin Tel Aviv da yankunan da ke kewaye da shi aƙalla sau biyu, yayin da tsarin kariya na Isra'ila ya gaza kakkabo makaman da aka harbo.
A cewar kafofin yaɗa labaran, gagarumin harin makaman linzami da na jirage marasa matuƙa na Iran ya yi sanadin ɗaukewar wutar lantarki da kuma kwashe dubban mazauna a Tel Aviv da kewaye.
Rahotannin sun ce an tilasta wa mazauna fiye da 4,000 ficewa daga gidajensu.
An tura jami'an lafiya da masu ba da agajin gaggawa na Isra'ila zuwa wurare takwas a faɗin Tel Aviv, yayin da wata babbar tashar jirgin ƙasa ta sami mummunar lalacewa.
Wace irin barna suka yi?
Magajin garin birnin Tel Aviv ya ce saboda waɗannan hare-haren, an dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a cikin birnin da kewaye har sai yadda hali ya yi.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Bugu da ƙari, garuruwa da dama da ke kusa da Tel Aviv sun rasa wutar lantarki bayan da makamai linzami na Iran suka faɗa musu.
Jaridar Times of Israel ta ce mutane guda biyu ne suka mutu lokacin da wani makami mai linzamin Iran ya faɗa garin Ramat Gan da ke kusa da Tel Aviv.
Iran ta harba sababbin makamai kan Isra'ila
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kakakin dakarun sojojin Iran ya bayyana cewa a kwanakin nan rundunoninsu suna amfani da manyan makamai na zamani waɗanda ba su taɓa amfani da su ba a baya.

Source: Getty Images
Rundunar sojojin ta ce ta farmaki filin jirgin sama na Ben Gurion da jirage marasa matuƙa, inda aka jibge jiragen dakarun Isra'ila masu loda man fetur a sararin samaniya.
Hakazalika ta bayyana cewa, don tunawa da sojojin da suka yi shahada a cikin jirgin ruwan yaƙi na Dena, tare da shahidi Ali Larijani, da kuma shahidi Janar Qolamreza Soleimani, ta harba tarin jiragen marasa matuƙa zuwa filin jirgin sama na Ben Gurion inda gwamnatin Isra'ila ke ajiye jirajenta na loda mai.
Haka kuma rundunar sojin ta gode wa al'ummar Iran saboda gagarumin fitowar da suka yi yayin jana'izar sojojin ruwan na jirgin Dena.
Iran ta cafke masu taimakon Amurka, Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukunta a Iran sun cafke mutane da dama wadanda ake zargi da aikata laifuffukan cin amanar kasa.
Hakazalika, mahakuntan sun bayyana gudanar da ayyukan kakkabe mutanen da suka bayyana a matsayin “maci amana” waɗanda ke mara wa muradun Amurka da Isra'ila baya.
An bayyana cewa mutanen da aka kama suna shirin kaddamar da ayyukan nuna adawa da tsarin mulkin addini na ƙasar.
Asali: Legit.ng

