Oman Ta Saba Wa Saudiyya da Najeriya, Ta Fitar da Sanarwa kan Watan Karamar Sallah
- Oman ta nemi al'ummmar musulmin kasar su fara duban jinjirin watan karamar Sallah watau Shawwal, 1447AH daga ranar Alhamis mai zuwa
- Kasar dai na daya daga cikin kasashen da suka saba da kasashe kamar Saudiyya da Najeriya tun lokacin daukar azumin farko na Ramadan
- Kwamitin da ke kula da harkokin ganin wata a Oman ya bukaci jama'a da suka kai rahoto idan sun ga jinjirin watan a ranar Alhamis, 29 ga Ramadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oman - Hukumomin kasar Oman sun fitar da sanarwa game da duban jinjirin watan Karamar Sallah, wata na 10 a kalandar addinin musulunci.
Kwamitin da ke kula da harkokin ganin wata na Oman ya yi kira ga musulmai yan kasar su fita su fara duban jinjirin watan Shawwal, 1447AH daga ranar Alhamis, 29 ga watan Ramadan, wanda ya yi daidai da 19 ga Maris, 2026.

Source: Twitter
Rahoton Gulf News ya nuna cewa Oman za ta fara duba jinjirin watan Sallah ne a ranar Alhamis, sabanin wasu kasashe kamar Najeriya da Saudiyya, inda za a fara duban watan yau Laraba.
Legit Hausa ta fahimci cewa Oman na daya daga cikin kasashen da suka fara azumi a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu, 2026, ma'ana dai ba su fara azumi rana daya da Saudiyya ba.
Hukumomin Oman sun bukaci ‘yan kasa da mazauna kasar da su rika sa ido domin neman ganin jinjirin watan, tare da kai rahoton duk wata sahihiyar gani ga kwamitocin da suka dace.
Wannan mataki na da muhimmanci matuka domin shi ne zai tabbatar da karshen watan azumin Ramadan da kuma fara bikin karamar Sallah, wato Eid al-Fitr.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Oman ya wallafa a shafinsa na X, ya ce:
"Babban Kwamitin Ganin Wata fita a yammacin Alhamis, domin fara duban jinjirin watan Shawwal na shekara ta 1447 AH. Kwamitin yana kira ga 'yan ƙasa da mazauna da su sa ido su nemi watan karamar Sallah.

Kara karanta wannan
Azumi ya zo karshe, Sarkin Musulmi ya fitar sanarwa kan ranar karamar Sallah a Najeriya
Qatar ma ta shiga sahun fara duban wata
A kasar Qatar, Kwamitin Ganin Wata da ke karkashin Ma’aikatar Kula da Harkokin Addini (Awqaf) ya yi kira ga musulmi da su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Laraba, 18 ga Maris, 2026.
A cikin wata sanarwa, kwamitin ya bukaci duk wanda ya ga jinjirin wata da ya garzaya zuwa hedikwatar ma’aikatar Awqaf da ke yankin Al Dafna domin bayar da shaida.
An kuma bayyana cewa kwamitin zai yi zama bayan sallar Magariba domin sauraron shaidu da kuma yanke hukunci kan ranar karamar Sallah.
Yaushe za a duba wata a Najeriya?
A Najeriya, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci a fara duban jinjirin watan Shawwal daga gobe Laraba, 29 ga Ramadan, 1447AH.
Ya bukaci duk wanda ya ga jinjirin watan ya kai rahoton ganin sa ga Hakimi ko Mai Unguwa mafi kusa da shi, domin isar da sakon ga Majalisar Sarkin Musulmi don tabbatarwa.
Fadar Sarkin Musulmi ta kuma bayar da wasu lambobin waya na musamman domin kai rahoton ganin jinjirin wata kai tsaye ga ofishin kwamitin ganin wata.
Asali: Legit.ng
