Kasashen Musulmi Sun Kira Taron Gaggawa saboda Yakin Iran da Amurka
- Yayin da yakin da Isra'ila da Amurka hada kai suka kaddamar a Iran ke cigaba da jawo asarar rayuka, shugabannin Musulmi za su yi zama
- Ma'aikatar harkokin kasar Saudiyya ta bayyana cewa a yau 29 ga watan Ramadan, 1447 za yi zaman a babban birnin kasar, Riyadh
- Ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana cewa zai halarci zaman tare da sanar da wasu muhimman abubuwan da za su tattauna a tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Shugabannin kasashen Musulmi sun fara yunkurin shawo kan yakin da ya barke a Gabas ta Tsakiya bayan harin Amurka/Isra'ila a kan Iran.
Kasar Saudiyya ta sanar da lokaci da wajen da shugabannin za su zauna domin lalubo hanyar warware rikcin da ya shiga mako na uku.

Source: Getty Images
Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta yi karin bayani game da manufar taron da za su yi a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.
Iran: Kasashen Musulmi za su yi taro
Kasar Saudiyya ta bayyana cewa ita za ta karbi bakuncin babban taron kasashen Larabawa da na Musulmi da za a yi a birnin Riyadh a yau.
Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce:
"Masarautar Saudiyya za ta karbi bakuncin wani taron ministocin harkokin wajen kasashe a birnin Riyadh a wannan yammaci na ranar Laraba, 29 ga Ramadan 1447AH, wanda ya yi daidai da 18 ga Maris 2026.
"Taron zai kasance tsakanin ministocin harkokin wajen wasu kasashen Larabawa da na Musulmi, da nufin kara tuntuba kan hanyoyin inganta tsaro da zaman lafiyar yankin."
Turkiyya za ta halarci taron Musulmi
Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai halarci taron da Saudiyya za ta jagoranta a Riyadh dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin, kamar yadda wata sanarwa ta hukuma ta bayyana a ranar Laraba.
Rahoton Anadolu Agency ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta ce za a gudanar da taron a ranar Laraba a babban birnin Saudiyya, Riyadh.
Ta kara da cewa taron zai mayar da hankali ne kan sababin abubuwan da ke faruwa a yankin, ba tare da bayyana cikakkun bayanai kan ajandar taron ko kasashen da za su halarta ba.

Source: Getty Images
Tashin hankula a Gabas ta Tsakiya sun karu tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hari na hadin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Iran ta mayar da martani da harba jirage marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra’ila, tare da kai hari a Jordan, Iraq da kasashen yankin Gulf.
Sultan ya caccaki Amurka/Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana kan hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran a karshen watan Fabrairun 2026.
Ya bayyana cewa an kai hare-hare kasashen Musulmi da dama a baya kamar Libya, Iraq, Sudan da sauransu, lamarin da ya jefa su a matsala.
Sultan ya kara da cewa kai irin harin ya saba dokar kasa da kasa tare da cewa Iran tana da hakkin kare kanta daga duk wata barazana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

