Iran Ta Magantu Kan Hari a Cibiyar Nukiliyarta, Ta Fadi Halin da Wurin ke Ciki

Iran Ta Magantu Kan Hari a Cibiyar Nukiliyarta, Ta Fadi Halin da Wurin ke Ciki

  • Babbar Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta ce an harba makami a tashar nukiliyar Iran a ranar Talata
  • An kai harin ne a tashar nukiliya ta Bushehr wadda ita ce kadai ke aiki a Iran yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya
  • Shugaban IAEA ya bukaci a yi taka-tsantsan domin kauce wa hadarin nukiliya yayin rikicin da ake yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya 'International Atomic Energy Agency' ta yi magana kan hari a Iran.

Hukumar ta bayyana cewa hukumomin Iran sun sanar da cewa an harba wani makami zuwa tashar nukiliya ta kasar.

An kai hari cibiyar nukiliya a Iran
Cibiyar nukiliyar Bushehr a Iran da Shugaba Masoud Pezeshkian. Hoto: BEHROUZ MEHRI/AFP, Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

An ce makamin ya fadi ne a harabar tashar nukiliya ta Bushehr a ranar Talata 17 ga watan Maris, 2026 da dare, amma babu wata barna da aka samu, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Amurka, Isra'ila sun far wa Iran da yaki

Hakan na zuwa ne bayan sake barkewar yaki tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.

Harin ya yi sanadiyyar rasa ran jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei a ranar Asabar 28 ga watan Fabrurairun shekarar 2026.

Trump ya sha nanata cewa akwai barazana game da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya a Gabas ta Tsakiya da duniya baki daya.

Ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne hana Iran mallakar makamin nukiliya, yana gargadin cewa hakan zai iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin haɗari.

Ya kuma bayyana cewa an lalata rundunar ruwan Iran, amma har yanzu jiragen dakon mai sun kasa wucewa ta mashigan Hormuz saboda tsoron nakiyoyi.

Trump ya magantu kan mallakar nukiliyar Iran
Shugaba Donald Trump yayin kamfe a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Babu jikkata ko rasa rai da aka samu

Hukumar ta kara da cewa babu wani ma’aikaci da ya jikkata sakamakon wannan lamari.

Shugaban hukumar, Rafael Grossi, ya bukaci bangarorin da ke rikici su yi taka-tsantsan domin kauce wa hadarin fashewar nukiliya.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Tashar Bushehr ita ce kadai tashar nukiliya mai aiki a Iran, kuma an fara hada ta da wutar lantarki tun shekarar 2011.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ci gaba tsakanin Iran da isra’ila tare da goyon bayan Amurka.

Tun shekarar 2018, Iran ke fuskantar takunkumin Amurka bayan janyewar kasar daga yarjejeniyar nukiliya, cewar NDTV World.

Sai dai Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kawai, ba domin kera makaman nukiliya ba domin zama barazana ga wasu kasashe ba.

Trump ya fara kosa wa kan yakin Iran/Isra'ila

Kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tasirin da yakin Iran da Isra'ila ke yi kan farashin mai a duniya.

Trump ya ce farashin mai zai ragu sosai bayan yaƙin Iran ya ƙare, duk da tsadar man fetur da ake fama da ita yanzu dalilin yakin da ake yi.

Yaƙin da ake yi da Iran ya haifar da tashin farashin mai, yayin da jiragen dakon mai suka makale a mashigan Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.