Ban da Hare Haren Iran, An Gano Wata Barazana da Sojojin Amurka Ke Fuskanta a Gabas
- Banda hare-haren da Iran take kai wa kan sansanonin Amurka a kasashen Gulf, dakarun na kuma fuskantar wasu hare-hare daga Saraya Awliya al-Dam
- Kungiyar mayakan sa-kai ta Saraya Awliya al-Dam ta ce ta kai hare-hare har guda 50 ga sansanonin Amurka ta hanyar harba makamai da jirage marasa matuka
- Rundunar sojin Iran (IRGC), ta yi ikirarin cewa hatta jirgin saman dakon man fetur na Amurka (KC-135), ya fado ne bayan harin kungiyar a Iraki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iraƙi - Wata ƙungiyar mayakan sa-kai ta ƙasar Iraƙi mai suna Saraya Awliya al-Dam ta fitar da hare-haren da ta kai kan wurare, musamman sansanonin Amurka a cikin kwanaki 15 da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa ta ƙaddamar da hare-hare har guda 50 ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin Amurka dake yankin Kurdistan a arewacin Iraƙi.

Kara karanta wannan
Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Source: Getty Images
Sojojin Amurka na fuskantar hare-hare daga Saraya
Haka zalika, ƙungiyar ta bayyana cewa ta kai hare-hare guda 21 kan sansanin Victoria Camp dake Bagadaza, da wasu hare-hare 11 kan dakarun Amurka dake ƙasar Siriya, a cewar rahoton Alhazeera.
Kazalika, ta ce ta kai wasu hare-haren jirage marasa matuka guda 28 a sassan ƙasashen Saudiyya, Kuwait, da Jordan.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta kai waɗannan hare-hare ne domin ɗaukar fansar kisan tsohon jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da dakarun Amurka da Isra'ila suka yi.
Baya ga hare-haren da Iran take kai wa kan sansanonin Amurka a kasashen Gulf, dakarun suna kuma fuskantar barazanar hare-hare daga Saraya Awliya al-Dam.
Batu kan jirgin Amurka da ya faɗo a Iraƙi
A daidai lokacin da waɗannan iƙirarin ke fitowa, rundunar tsaron Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da mutuwar dukkan jami'ai shida dake cikin jirgin dakon man fetur na Amurka (KC-135) wanda ya yi hatsari a yammacin Iraƙi ranar 12 ga Maris.
To sai dai kuma, an samu saɓanin rahoto tsakanin Amurka da Iran game da abin da ya haddasa hatsarin:
- Rahoton CENTCOM: Amurka ta ce har yanzu ana bincike kan hatsarin, amma ta tabbatar da cewa ba harbin makiya ne ya kakkabo jirgin ba.
- Rahoton Iran (IRGC): Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran da rundunar IRGC sun yi iƙirarin cewa dakarun gwagwarmaya na yammacin Iraƙi ne suka harbo jirgin na Boeing KC-135 Stratotanker da makami mai linzami yayin da yake loda wa wani jirgin yaƙi mai.

Source: Getty Images
Kungiyar da ke barazana ga sojojin Amurka
Wannan ƙungiya ta Saraya Awliya al-Dam, wadda ta fara aiki tun bayan mamayar Amurka a shekarar 2003, tana ɗaya daga cikin ƙungiyoyin mayakan sa-kai na Shi'a dake fafatawa a yankin.
Rahoton da Economic Times ta fitar ya tabbatar da cewa hare-haren da Saraya Awliya al-Dam ta ke kai wa sun shafi wurare da dama ciki har da filin jirgin saman Bagadaza da birnin Erbil.
Daraktan tsaro a Amurka ya yi murabus

Kara karanta wannan
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta tsoma baki game da harin Iran kan kasashen Larabawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Joseph Kent ya yi murabus daga mukaminsa na Shugaban cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Amurka, kan yadda Donald Trump ke yaki da Iran.
Tsohon daraktan ya zargi gwamnatin Trump da fara yaƙi da Iran sakamakon matsin lambar da ta samu daga ƙasar Isra'ila da wasu masu fada a ji.
A cikin wasiƙar da ya aika wa Trump, Kent ya gargaɗi Amurka cewa yaƙin Iran wata makarkashiya ce da aka shirya, kamar yadda aka yi a Iraki.
Asali: Legit.ng
