Malami Ya Saba da Netanyahu, Ya Shawarci Musulmi kan Sallar Idi a Masallacin Kudus
- Wani malamin addini, Sheikh Ekrima Sabri, ya fitar da fatawa kan sallar idi a masallacin Kudus wanda aka rufe tun farkon fara yaki
- Malamin ya yi kira ga Musulmi su gudanar da sallar Idi kusa da masallacin Kudus duk da rufe shi a aka yi a farkon Ramadan
- Fatawar ta bukaci jama’a su nufi yankin masallacin su yi sallah kusa da shi, tare da rufe sauran masallatai a Jerusalem
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jerusalem, Israel - Malamin addini kuma limamin Masallacin Kudus, Sheikh Ekrima Sabri, ya fitar da wata fatawa kan sallar ido a masallacin Kudus.
Malamin ya yi kira ga Musulmi su gudanar da sallar Idi kusa da masallacin, bayan rufe shi da aka yi a farkon azumin Ramadan.

Source: Getty Images
Rahoton Middle East Monitor ta ruwaito cewa an rufe masallacin ne saboda fargabar tsaro wanda aka hana salla a Ramadan.

Kara karanta wannan
Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri
Yadda aka zargi Sheikh Sabri a Isra'ila
Limamin masallacin ya sha jawo maganganu a yankin wanda har ya jawo aka tuhume shi da neman tayar da tarzoma a ƙarshen shekarar 2025.
Limamin Masallacin, Sheikh Ekrima Sabri, ya bayyana a gaban wata kotun Isra’ila bisa zargin tunzura jama’a a yankin.
An shigar da tuhumar ne daga masu gabatar da kara na Isra’ila a watan Agustan 2024, wanda ya shafi jawabai biyu na ta’aziyya da malamin ya yi a shekarar 2022.
Har ila yau, ya yi ta'aziyya ga tsohon shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, wanda aka kashe a babban birnin Tehran a 2024. An karanta takardar tuhumar da ake yi wa limamin a zaman kotun Magistrate da ke Jerusalem, cewar TRT World.
Sheikh Ekrima Sabri mai shekaru 87, ya je kotu a kan keken guragu tare da lauyoyinsa da kuma wasu magoya bayan Falasɗinawa.
Ya ce hukumomin Isra’ila na ƙoƙarin yaɗa tsoro a tsakanin Falasɗinawa domin raunana juriyarsu.

Source: Getty Images
Kiran da Sheikh Sabri ya yi ga Musulmi
Majiyoyi daga Falasdinu sun ce an bukaci dukkan Musulmi su nufi yankin masallacin Kudus su yi sallah kusa da shi, tare da dakatar da sallah a sauran masallatan Jerusalem.
Sojojin Isra’ila sun hana masu ibada gudanar da salla a darare masu albarka na Ramadan inda aka tilasta wa daruruwan mutane yin ibada a wajen katangar harabar masallacin cikin tsaro mai tsauri.
Masu ibada sun gudanar da sallolin Isha’i da Tarawihi a tituna kusa da Bab al-Sahira da Bab al-Amud, yayin da aka kakaba kulle da tsauraran bincike ga mazauna yankin.
Kasashen Musulmi sun soki rufe masallacin Kudus
Mun ba ku labarin cewa wasu kasashen Musulmi da Larabawa takwas sun soki Israel kan rufe Masallacin Al-Aqsa a Jerusalem yayin watan Ramadan.
Ministocin harkokin wajen kasashen sun ce hana shiga masallacin ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma tsokana ce ga masu ibada.
Sun bukaci gwamnatin Benjamin Netanyahu ta bude wuraren ibada a tsohon birnin Jerusalem a Isra'ila nan take domin ci gaba da gudanar da ibada.
Asali: Legit.ng
