Trump Ya Yi Magana kan Amfani da Makamin Nukiliya a Yaki da Iran

Trump Ya Yi Magana kan Amfani da Makamin Nukiliya a Yaki da Iran

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya tattauna da manema labarai game da hare-haren da ake cigaba da kaiwa a Gabas ta Tsakiya a yaki da Iran
  • A hirar da ya yi, shugaba Trump ya amsa tambaya game da yiwuwar Isra'ila ta yi amfani da makaman nukiliya a Iran idan yanayi ya jawo hakan
  • Hakan na zuwa ne bayan shiga mako na uku ana gwabza yaki tsakanin Amurka/Irsa'ila da Iran, lamarin da ke cigaba da jawo asarar rayukan fararen hula

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Yayin da yakin Iran da Amurka/Isra'ila ke kara daukar zafi, shugaban Donald Trump ya amsa tambayoyi daga 'yan jarida a fadar White House.

Wani dan jarida ya tambayi Trump kan ko Isra'ila za ta yi amfani da makamin nukiliya a kan Iran idan yakin ya ki ci ya ki cinyewa.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Donald Trump ya yanke lokacin da yakin Iran da Isra'ila zai kare

Shugaba Donald Trump a kasar Amurka
Shugaba Donald Trump yana yi wa Amurkawa jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton the Hill ya nuna cewa Donald Trump ya kara da cewa Amurka ta yi nasara bayan gama amsa tambayoyin da aka gabatar masa.

Maganar Trump kan harba nukiliya Iran

Shugaba Donald Trump ya jaddada cewa Isra’ila ba za ta yi amfani da makamin nukiliya a kan Iran ba, bayan da aka tambaye shi kan gargadin da daya daga cikin masu ba shi shawara ya yi.

“Isra’ila ba za ta yi haka ba. Ba za ta taba yin haka ba,”

Inji Trump yayin da yake ganawa da manema labarai a dakin East Room na Fadar White House.

Maganar tsananta yaki da Iran

Rahoton CBS ya nuna cewa an tambayi Trump dangane da wasu kalamai da hadimi a gwamnatinsa, David Sacks, ya yi, inda ya yi gargadi kan “haduran” da ke tattare da kara tsananta yakin Iran.

“Isra’ila na iya fuskantar babbar barna,”

Inji Sacks a wata tattaunawa.

Kara karanta wannan

To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

“Sannan kuma akwai yiwuwar ta kara tsananta yakin ta hanyar tunanin amfani da makamin nukiliya.”

A martanin da ya yi, shugaba Donald Trump ya bayyana cewa David Sacks bai taba gabatar masa da wannan ra’ayi kai tsaye ba.

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Iran, wadanda suka fara a karshen watan da ya gabata.

Isra'ila za ta kara kai hare-hare

Rundunar tsaron Isra’ila ta bayyana a ranar Lahadi cewa tana shirin ci gaba da kai hare-hare kan Iran na akalla karin makonni uku.

Benjamin Netanyahu na kasar Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Effie Defrin, ya bayyana a wata hira cewa Isra’ila na da dubban wurare da take shirin kai wa hari.

Iran ta raunata sojojin Amurka 200

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Amurka ta tabbatar da raunata wasu daga cikin dakarun sojojinta sama da 200 a hare-haren Iran.

Sojojin sun samu rauni ne a hare-haren da aka kai kasashen Larabawa bakwai da suka hada da Saudiyya, Qatar, Bahrain da sauransu.

Wani kwamandan sojojin Amurka ne ya bayyana haka, inda ya ce wasu daga cikin sojojin sun fara samun sauki kuma sun koma bakin aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng