Amurka Ta Kira Ruwa, Iran Ta Bayyana Babban Tanadin da Ta Yi Mata
- Mahukunta a birnin Tehran na ci gaba da jimamin nutsar da jirgin ruwan yakin Iran da Amurka ta yi a cikin teku
- Babban kwamandan rundunar sojojin ruwan Iran, Rear Admiral Shahram Irani, ya bayyana cewa ana ci gaba da bakin ciki kan kisan da aka yi wa sojojin da ke jirgin
- Ya bayyana cewa kisan da aka yi wa sojojin ruwan ba zai tafi a banza ba domin akwai shirin da suka yi na daukar fansa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Kwamandan rundunar sojojin ruwan Iran, Rear Admiral Shahram Irani, ya sha alwashi kan nutsar da jirgin ruwan yakin Iran da Amurka ta yi.
Shahram Irani ya bayyana cewa makiya Iran za su fuskanci martani mai zafi sakamakon kisan aƙalla sojojin ruwa 87 a kusa da gabar Sri Lanka da ke tekun Indiya.

Source: Twitter
Kwamandan rundunar sojojin ruwan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Press Tv ta kasar Iran.
Wane alwashi kasar Iran ta sha?
“Ba za mu manta da laifin da maƙiyi ya yi ba, kuma za mu ɗauki fansar jinin shahidanmu."
"Ya kamata maƙiyi ya sani cewa za mu hukunta shi da munanan hare-hare daga inda ba ya tsammani.”
Rear Admiral Shahram Irani
Iran ta yi bakin cikin nutsar da jirgin ruwanta
Rear Admiral Shahram Irani ya bayyana cewa al'ummar ƙasar na cikin baƙin ciki sakamakon wannan babban rashi, amma ya jaddada ƙudurin sojojin Iran na ganin sun ɗauki fansar jinin shahidan.
“Kodayake yau muna kukan masoyanmu, amma da ikon Allah, mun durƙusar da maƙiyi."
- Rear Admiral Shahram Irani
Amurka ta nutsar da jirgin Iran a teku
A ranar 4 ga Maris, wani babban jirgin ruwan yaƙi na Amurka mai tafiya a karkashin teku ya harba makamin torpedo ka jirgin ruwan Iran mai suna IRIS Dena, inda ya nutsar da shi a gabar tekun Galle da ke Sri Lanka.
An ceto kusan sojojin ruwa 32, yayin da wasu da dama har yanzu ba a gansu ba.
Kimanin ma'aikata 104 ne suka yi shahada a wannan harin ta'addanci, inda aka gano gawarwaki 87 sannan aka ceto sojoji 32.

Source: Getty Images
Rundunar sojojin ruwan Indiya ce ta gayyaci IRIS Dena a hukumance don shiga cikin wani atisayen haɗin gwiwa kafin dakarun ruwan Amurka su farmako jirgin da hari a cikin ruwan ƙasa da ƙasa, a daidai lokacin da ake tsaka da yaƙi da al'ummar Iran.
Jirgin ruwan yakin na Amurka ya farmaki IRIS Dena a cikin ruwan ƙasa da ƙasa yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Iran bayan ya halarci atisayen hadin gwiwa da ƙasar Indiya.
An shirya gudanar da jana'izar sojojin ruwan na Iran a ranar Laraba, yayin da ake sa ran gudanar da bukukuwan karramawa da juyayi a ranar Talata.
Trump ya yi mamakin martanin Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kadu kan hare-haren daukar fansa na Iran.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Donald Trump ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda ta rika kai hare-haren daukar fansa kan sansanonin sojojin Amurka da ke kasashe makwabta.
Shugaba Trump ya bayyana mamakinsa game da hare-haren fansar da Iran ta kai wa ƙasashen yankin Gulf da ke kewaye da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

