Ana cikin Yaki da Iran, Shugabar Ma'aikatan Fadar Trump Ta Kamu da Babbar Cuta
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa wata ta kusa da shi a gwamnati ta kamu da cuta
- Donald Trump ya bayyana cewa shugabar ma'aikatan fadar White House, Susie Wiles, ta kamu da cuta amma za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta
- Shugaban kasar na Amurka ya yaba da juriyar Susie Wiles wadda ta kasance mace ta farko da ta taba rike mukamin shugabar ma'aikatan fadar White House
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, shugabar ma'aikatan fadar White House, Susie Wiles, ta kamu da cuta.
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa an gano Susie Wiles tana ɗauke da cutar kansar nono a matakin farko.

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin Truth Social, a ranar Litinin, 16 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan
Iran ta sake jikawa Amurka aiki, ta ruguza shirin Shugaba Trump ana tsaka da musayar wuta
Susie Wiles ta kamu da cutar kansa
Trump ya rubuta cewa yanayin jinyar Susie Wiles yana da "kyau ƙwarai" kuma za ta ci gaba da aikinta a fadar White House yayin da take karɓar magani.
“Kuzarinta da kuma ƙudurinta na ci gaba da gudanar da aikin da take so, kuma take yin sa yadda ya kamata, yayin da take jinya, ya nuna muku dukkan abin da kuke buƙatar sani game da ita."
- Shugaba Donald Trump
Susie Wiles za ta ci gaba da aiki
Tashar CNN ta ce a cikin wata sanarwa, Susie Wiles, ta bayyana cewa tana shirin ci gaba da gudanar da aikinta na shugabar ma'aikatan fadar White House.
“Ina godiya da samun ƙwararrun likitoci waɗanda suka gano kansar tun da wuri kuma suke jagorantar kulawa da ni, kuma ina ƙarfafa gwiwa da yanayin samun sauƙi mai kyau da ake sa ran samu."
- Susie Wiles
Ta yi aiki tare da Donald Trump
Susie Wiles, wadda ta kasance jigo a kusa da Trump cikin 'yan shekarun nan, ta taimaka wajen jagorantar nasarar yaƙin neman zaɓensa na 2024 kafin ta shiga fadar White House a matsayin shugabar ma'aikata.
Wannan naɗin ya sa ta zama mace ta farko da ta taɓa riƙe wannan muƙamin.
Tun daga wannan lokacin, Wiles ta yi ƙoƙarin gudanar da ayyukan yau da kullum a cikin fadar, yayin da ta ba Trump damar yin ayyukansa ba tare da matsin lamba ba.

Source: Getty Images
Baya ga kansar fata, kansar nono ita ce mafi yawan nau'in kansa a tsakanin mata a Amurka.
Mafi yawanci tana faruwa ne ga mata masu matsakaicin shekaru da waɗanda suka tsufa; shekaru 62 ne matsakaicin shekarun da ake gano cutar.
Magani ya dogara ne da nau'in kansar maman da kuma matakin da ta kai, amma yana iya haɗawa da tiyata, chemotherapy da sauransu.
Trump ya gargadi kasashen da ke cikin NATO
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi gargadi ga kasashen da ke cikin kawancen NATO.
Donald Trump ya gargade su kan cewa za su fuskanci matsala idan ba su taimaka wa Amurka wajen tabbatar da tsaron mashigar ruwan Hormuz ba.
Shugaba Trump ya kara da cewa ya kamata kasashen da ke amfana da jigilar man fetur da ke ratsa Tekun Fasha su taimaka wajen kare mashigin ruwan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
