Dubu Ta Cika: Ana cikin Musayar Wuta, An Kama Masu Yiwa Iran Zagon Kasa a Yaki da Amurka

Dubu Ta Cika: Ana cikin Musayar Wuta, An Kama Masu Yiwa Iran Zagon Kasa a Yaki da Amurka

  • Rundunar yan sandan Iran ta sanar da kama mutane kimanin 500 da ke munafurtar kasar wajen tura bayanai ga Isra'ila da Amurka
  • Wannan na zuwa ne bayan an shiga mako na uku da fara musayar wuta tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Isra'ila na amfani da bayanan da ta samu daga mutanen Iran wajen kai hare-hare

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Dakarun 'yan sandan kasar Iran sun damke mutane kimanin 500 da ake zargin da yi wa Amurka da Isra'ila leken asiri yayin da ake ci gaba da musayar wuta a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ‘yan sandan Iran, Ahmadreza Radan, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa jami’an tsaro sun kama mutane 500 da ake zargi da taimakawa abokan gabar ƙasar ta hanyar ba su bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi fariya, ta fadi nasarar da ta samu a kan fadar Ayatollah Khamenei

Yan sanda.
'Yan sanda na aikin ba da tsaro a tattakin da mutanen Iran suka fito don nuna goyon baya Hoto: ATTA KENARE
Source: Getty Images

Tribune Nigeria ta tattaro cewa matakin na zuwa ne yayin da jiragen yaƙin Isra'ila da na Amurka ke ci gaba da kai sababbin hare-haren sama a wurare daban-daban a cikin Iran.

Iran ta kama yan leken asiri 500

A cewar Radan, kusan rabin mutanen da aka kama suna da hannu a manyan laifuffuka, ciki har da ba da bayanan wuraren da ake kai hare-hare, ɗaukar bidiyo ko hotunan wuraren da aika waɗannan bayanai zuwa ƙasashen waje.

Ya ce wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun taimaka wajen gano muhimman wuraren soji da tsaro, wanda daga baya aka kai musu hare-hare.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Iran sun ce an kama daruruwan mutane a larduna daban-daban na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Yadda asirin 'yan leken asiri ya tonu

A Arewa maso Yammacin ƙasar, an ruwaito cewa mutane 20 aka kama bisa zargin aika bayanan wuraren sojoji da tsaro ga Isra’ila.

Kara karanta wannan

To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

A Arewa maso Gabashin Iran kuma, dubun wasu mutane 10 ya cika bisa zargin wasu daga cikinsu da tattara bayanai kan muhimman wuraren tattalin arziki da kayayyakin more rayuwa.

Mojtaba da Netanyahu.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iran ta gano shirin Amurka da Isra'ila

Hukumar leƙen asiri ta rundunar sojojin juyin juya hali na Iran ta ce Isra’ila da Amurka na ƙoƙarin tayar da tarzoma da amfani da ‘yan leƙen asiri domin haddasa rikici a cikin kasar.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Isra’ila ta fara kai hare-hare kan wuraren binciken tsaro a Iran, bayan samun bayanai daga wasu mutane a cikin ƙasar.

Iran ta fara harba makamin Sijjil zuwa Isra'ila

A baya, rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi amfani da makamai mai linzami mai hadarin gaske da ta kira da Sijjil a kan Isra'ila a jiya Lahadi.

Bayanai sun tabbatar da cewa Sijjil hatsabibin makami ne da Iran ta harba zuwa Isra'ila da zai iya zuwa Tel Aviv daga Tehran a minti bakwai.

Makamin Sijjil makami ne mai linzami mai matakai biyu da Iran ta kirkira kuma ta kera da kanta, kuma ana kiransa da wasu sunaye kamar Ashura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262