Bayan Trump Ya Nuna Damuwa, Faransa Ta Kira Iran kan Tsayar da Hare Hare

Bayan Trump Ya Nuna Damuwa, Faransa Ta Kira Iran kan Tsayar da Hare Hare

  • Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya kira shugabannin Iran ta wayar tarho bayan shiga mako na uku da fara yaki a Gabas ta Tsakiya
  • Emmanuel Macron ya bayyana cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi hare-haren da ake kaiwa kasashen Gabas ta Tsakiya da sauransu
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka, Donald Trump ya matsawa kasashen Turai lamba kan su kai masa dauki a yaki da Iran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce ya yi waya da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, inda ya bukace shi da ya dakatar da hare-hare da Iran ko kungiyoyin da ke mara mata baya ke kaiwa a Gabas ta Tsakiya.

Ya kara da cewa matakan da Faransa ke dauka a yankin na da manufar kare kai ne kawai, domin kare muradunta, kawayenta a yankin da kuma hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Trump ya harba bama bamai Iran, ya ce Amurka ta kai hari mafi muni a tarihi

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron
Emmanuel Macron a wani waje a birnin Paris. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Macron ya bayyana abubuwan da suka tattauna a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar 15 ga Maris, 2026 inda ya bayyana damuwar Faransa kan karuwar rikicin Gabas ta Tsakiya.

Abin da Emmanuel Macron ya fadawa Iran

Macron ya ce ya gargadi shugaban Iran kan illar da kara zafafa hare-haren soja a yankin zai iya haifarwa, tare da kira da a dakatar da duk wasu hare-hare da ake dangantawa da Tehran.

“Na bukace shi da ya kawo karshen hare-haren marasa karbuwa da Iran ke kai wa kasashen yankin, ko kai tsaye ko ta hannun kungiyoyin da ke mara mata baya, ciki har da a Lebanon da Iraq,”

- Inji Macron.

Shugaban Macron ya kuma jaddada cewa kasancewar Faransa a yankin na da manufar kare kai ne kawai, domin kare muradunta da kawayenta.

Bukatun Faransa ga kasar Iran

Shugaban Faransa ya kuma gabatar da wasu bukatu yayin tattaunawar, inda ya jaddada bukatar samar da wani sabon tsarin siyasa da tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

An fara kiran Tinubu ya ajiye Amurka a gefe, ya dauki darasi daga kasar Iran

“Sabon tsarin siyasa da tsaro ne kawai zai iya tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga kowa.
"Dole ne wannan tsarin ya tabbatar cewa Iran ba ta taba mallakar makaman nukiliya ba, sannan kuma ya magance barazanar da shirinta na makamai masu linzami da kuma ayyukan da ke haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin da duniya baki daya.”
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar Iran a wajen wani taro yana jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Nairametrics ya nuna cewa Macron ya kuma bukaci a maido da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci ta daya daga cikin muhimman hanyoyin ruwa na duniya.

Ya ce:

“Dole ne a maido da ‘yancin zirga-zirga ta mashigar ruwan Hormuz cikin gaggawa.”

An kashe sojan Faransa a Iraq

A wani labarin, kun ji cewa wani mummunan harin jirgi maras matuki da aka kai a Arewacin Iraq ya jawo mutuwar sojan Faransa da ke bakin aiki.

Rahotanni sun nuna cewa wasu sojoji shida sun ji rauni bayan jirgi maras matuki ya kai hari kan sansanin da sojojin Faransa ke ciki.

Sojoji na cikin kusan sojojin Faransa 600 da ke Iraq domin horas da dakarun kasar a matsayin wani bangare na kawancen kasa da kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng