An Gano Halin da Netanyahu Ke Ciki bayan Rade Radin Mutuwarsa a Harin Iran
- Tun makon da ya wuce aka yawaita rade-radin cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya mutu a hare-haren da Iran ta kai birnin Tel Aviv
- Bayan yawaita maganar jita-jitar mutuwar Netanyahu, kasar Isra'ila ta fitar da bidiyo da ya nuna halin da Firaministan ke ciki a halin yanzu
- Isra'ila da Amurka sun kaddamar da hare-hare a Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, abin da ya jawo mutuwar jagoran Iran, Ayatollah Khamenei
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - An samu bayanai game da halin da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ke ciki bayan jita-jitar mutuwarsa ta karade kafafen sada zumunta.
An yawaita yada jita-jitar mutuwar Netanyahu ne bayan fitar da wani bidiyo da masu sharhi suka ce da fasahar AI aka hada shi, inda suka ce ya bayyana da yatsu shida maimakon biyar.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

Source: Getty Images
A kokarin fadar halin da Benjamin Netanyahu ke ciki, tashar Al-Jazeera ta wallafa a Facebook cewa gwamnatin kasar Isra'ila ta fitar da wani bidiyo.
Halin da Benjamin Netanyahu ke ciki
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya wallafa wani bidiyo a ranar Lahadi yana shan shayi tare da tattaunawa da hadiminsa, bayan jita-jitar da kafafen yada labarai suka yada cewa ya mutu ko ya ji rauni.
A cikin bidiyon da aka dauka a wani waje da ke birnin Jerusalem, wanda aka wallafa a kafafen sada zumunta, hadimin nasa ya tambaye shi game da jita-jitar.
Netanyahu ya mayar da martani da wata magana ta barkwanci kan kalmar “mutu,” wadda a harshen Ibrananci ake amfani da ita wajen nuna mutum yana matukar son wani abu.
Yayin da yake daukar kofin shayi, ya ce:
“Ina matukar son shayi. Kuma ka san me? Ina matukar son mutanena,”

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu
An tantance bidiyon Netanyahu
Kamfanin labarai na Reuters ya tabbatar da wurin da aka dauki bidiyon Netanyahu ta hanyar kwatanta shi da hotunan baya na wajen, wadanda suka yi daidai da abin da ke cikin bidiyon.
Haka kuma an tabbatar da ranar ta hanyar wasu bidiyo da hotuna daga wajen da Isra'ila ta wallafa a ranar Lahadi, 15 ga watan Maris 2026.
Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, Netanyahu ya ziyarci akalla garuruwa biyu da dakarun Iran suka kai hari, da kuma wani asibiti, tashar jiragen ruwa da sansanonin soji.

Source: UGC
Sai dai ba a bai wa kafafen yada labarai damar bin wadannan ziyara sosai ba, domin ofishinsa ne ke tura bidiyon, lamari da ya jawo karuwar jita-jitar mutuwarsa.
Ga bidiyon Netanyahu da Al-Jazeera ta wallafa a X:
Iran ta harba makamin Sijjil Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Iran na cigaba da harba makamai masu linzami zuwa kasar Isra'ila, ciki har da makamin Sijjil mai hadarin gaske.
Rahotanni sun nuna cewa makamin Sijjil na da gudun gaske, inda aka ce zai iya tashi daga birnin Tehran zuwa Tel Aviv na Isra'ila a minti bakwai.
Binciken masana ya nuna cewa makamin nada nauyin gaske, inda aka bayyana cewa Iran ta fara kera shi ne tun farkon shekarun 1990.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
