Iran Ta Harba Babban Hatsabibin Makamin Sijjil zuwa Isra'ila a Karon Farko

Iran Ta Harba Babban Hatsabibin Makamin Sijjil zuwa Isra'ila a Karon Farko

  • Rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi amfani da makamai mai linzami mai hadarin gaske da ta kira da Sijjil a kan Isra'ila a ranar Lahadi
  • Masu bincike sun bayyana cewa makamin yana da gudun gaske, inda ya ke da karfin ikon zuwa Isra'ila daga Iran a cikin minti bakwai
  • Hakan na zuwa ne yayin da yakin da ake tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran ke cigaba da rincabewa ba tare da alamun tsagaita wuta ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Kasar Iran ta harba wasu manyan makamai masu linzami a ranar Lahadi da suka nufi wurare daban-daban a Isra’ila da kuma sansanonin sojin Amurka.

Cikin makaman da aka harba har da makamin Sijjil wanda aka yi amfani da shi karo na farko tun bayan fara yakin a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi matsalar da ta ke fuskanta yayin yaki da Iran

Samfurin makamin Sijjil na Iran
Samfurin makamin sijjil da Iran ta harba zuwa Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta harba makamin Sijjil Isra'ila

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa Sijjil hatsabibin makami ne da Iran ta harba zuwa Isra'ila da zai iya zuwa Tel Aviv daga Tehran a minti bakwai.

Makamin Sijjil makami ne mai linzami mai matakai biyu da Iran ta kirkira kuma ta kera da kanta, kuma ana kiransa da wasu sunaye kamar Ashura.

Bayani kan makamin Sijjil

Sijjil da Iran ta harba Isra'ila makami ne mai linzami mai kawuna biyu da ke amfani da man fetur, wanda ke iya kaiwa zuwa nisan kilomita 2,000, tare da iya ɗaukar nauyin kusan kilo 700.

Saboda ikon da yake da shi na yin motsi a sama yayin tafiya, an masa laƙabin “makami mai rawa”, domin yana iya kauce wa tsarin kariyar makamai masu linzami.

A cewar Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro da Kasa da Kasa (CSIS), makamin yana da tsawon kusan mita 18 kuma nauyinsa ya kai kimanin kilo 23,600.

Kara karanta wannan

To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

Tsarin amfani da man fetur yana ba shi wata muhimmiyar fa’ida ta soja, domin ana iya shirya shi da kuma harba shi cikin sauri fiye da tsofaffin makaman da Iran ke amfani da su kamar jerin makaman Shahab.

Yaushe Iran ta fara kera Sijjil

Rahoton da tashar ND TV ta wallafa sun nuna cewa Iran ta fara aikin kirkirar makamin Sijjil tun farkon shekarun 1990 domin shirin rana irin ta yau.

A cewar CSIS, gwajin farko na harba makamin ya faru ne a shekarar 2008, inda aka ce ya yi tafiyar kusan kilomita 800. An sake yin wani gwaji a watan Mayun 2009.

Mojtaba Khamenei kafin zama jagoran Iran
Sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tun daga 2009 an gudanar da wasu gwaje-gwaje guda hudu. A gwaji na shida kuwa, an ce makamin ya yi tafiyar kusan kilomita 1,900 zuwa Tekun Indiya.

Iran ta harba makamai Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta harba wasu makamai masu linzami sansanin sojojin Amurka a wani yanki na kasar Saudiyya.

An samu bayanai cewa harin ya yi barna sosai, inda ya yi nasarar lalata wasu manyan jiragen da Amurka ke amfani da su wajen jigila.

Wasu rahotanni sun nuna cewa tun a kwanakin baya hare-haren Iran sun lalata wasu daga cikin jiragen Amurka da ke Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng