Tirkashi: Abin da Zai Faru da Amurka idan Ta Kashe Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya nuna yiwuwar kasarsa ta iya kashe sabon jagoran addini na Iran da aka nada, Mojtaba Khamenei
- Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya aika da sakon gargadi ga Amurka kan kada ta yi kuskuren kashe Mojtaba Khamenei wanda aka ce ya samu raunuka
- Kazem Jalali ya ce mutanen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cike suke da fushi da bukatar daukar fansa kan kisan da aka yi wa Ayatollah Ali Khamenei
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya ja kunnen Amurka kan kashe sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei.
Kazem Jalali ya yi gargadin cewa Amurka za ta fuskanci martani mai tsanani idan ta yi ƙoƙarin kashe sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei.

Source: Twitter
Jakadan na Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Sputnik.
Iran ta gargadi Amurka kan taba Mojtaba Khamenei
Lokacin da aka tambaye shi ko wane irin martani Iran za ta mayar idan Amurka da Isra'ila suka yi yunƙurin kashe sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei, Kazem Jalali ya ce:
"Kuna ganin martanin Iran a yau. Muna son ɗaukar fansar jini ne saboda jagoranmu [Ayatollah Ali Khamenei]."
"Jama'a suna cikin fushi kuma suna buƙatar ɗaukar fansa kan jinin da aka zubar. Babu shakka, Amurkawa sun fuskanci martani mai tsanani, kuma za su ci gaba da fuskantarsa a nan gaba."
- Kazem Jalali
Amurka da Isra'ila sun kashe Ayatollah Khamenei
A ranar 28 ga Fabrairun 2026 Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan wasu wurare a Iran, ciki har da Tehran, wanda ya janyo ɓarna da asarar rayukan fararen hula.
Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan yankunan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Trump ya fadi halin da Mojtaba Khamenei ke ciki bayan harin Isra'ila
Tun farko Amurka da Isra'ila sun yi iƙirarin cewa harin nasu na ya zama dole ne don dakile barazanar da suke gani daga shirin nukiliyar Iran, amma ba da daɗewa ba suka fito fili cewa suna son ganin an canza gwamnati a Iran.
An kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei a ranar farko da aka fara kai hare-haren.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ayyana kwanaki 40 na zaman makoki saboda kisan da aka yi wa Ayatollh Khamenei mai shekaru 86.
Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifinsa
A ranar 8 ga Maris 2026, aka naɗa ɗansa Mojtaba Khamenei, wanda har yanzu bai fito fili ba, a matsayin magajinsa.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce sabon Jagoran na Iran ya ji rauni amma yana jin sauƙi a yanzu.
Trump ya fadi bukatar da Iran ke nema
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa sun samu nasara kan Iran a yakin da ake yi.
Donald Trump ya bayyana cewa an yi gagarumar nasara kan Iran a yaƙin da Amurka da Isra’ila suke yi da ita.
Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa Iran na son wata yarjejeniya da shi ba zai amince da ita ba kwata-kwata.
Asali: Legit.ng
